Kanun Labaru: Daga Litinin 5 Zuwa Alhamis 8 Ga Watan Safar 1443

Buhari

LAHADI 11 Ga Safar (19/09/21)

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Lahadi,  goma sha daya ga watan Safar,  shekarar 1443 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta,  Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da goma sha tara ga watan Satumba,  shekarar 2021.

A Lahadin nan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa Newyork/Niyok ta Amurka,  don halartar wani taro na 76, na Majalisar Dinkin Duniya.

Likitocin da ke yajin aiki har kotun sasanta lamuran ma’aikata ta umarta su koma aiki, sun ce ba su gamsu da wannan hukunci ba, za su daukaka kara gaba.

Wasu mutanen jihar Zamfara sun nuna rashin amincewrsu da batun kara tsawon dokar katse hanyoyin sadarwa ta waya da dakatar da cin kasuwanni na mako-mako.

‘Yan sanda a jihar Zamfara, sun ceto wasu mutanen Jihar Katsina su 20,  da suka haura wata hudu a hannun kidinafas a jihar.

Sojoji sun ceto Manjo Datong da kidinafas suka yi kidinafin a kwalejin horas da kananan hafsoshin soja da ke Kaduna.

LITININ 12 Ga Safar (20/09/21)

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa Newyork ta kasar Amurka,  don halartar wani taro na Majalisar Dinkin Duniya na 76 da za a fara gobe Talata.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada wakilan hukumar kamfanin mai na kasa NNPC.

Kungiyar SERAP mai rajin kare hakkin bil’Adama da bunkasa tattalin arziki,  ta roki shugabannin majalisar dokoki ta kasa kada su amince wa shugaban kasa bukatar da ya mika musu ta sake ciwo/ciyo wani bashin.

Oni na Ofe Oba Adeyeye,  ya killace kansa na kwana bakwai don yi wa kasar nan addu’a.

Wasu ‘yan fashin daji sun kashe mutum shida a Tangaza ta jihar Sakkwato,  a ta daya bangaren wasu fusatatttu a jihar Sakkwato sun banka wa wasu ‘yan fashin daji wuta suka kashe su.

Hukumar NJC ta al’amuran masu shari’a ta ba da shawarar nadin jami’an shari’a su 36.

TALATA 13 Ga Safar (21/09/21)

Gwamnonin Arewa na makokin rashin da aka yi na tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Nijeriya Obadiah Mailafiya.

Kungiyar Daliban Nijeriya ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kara himma wajen kare ‘yan makaranta da ke karatu a manyan makarantun kasar nan.

‘Yan Sanda da suka yi ritaya, sun yi wata zanga-zanga a Kaduna, a kan kudadensu na fansho.  Sun kuma nemi a cire su daga tsarin nan na fansho na karo-karo tsakanin gwamnati da ma’aikaci.

Wata kungiya ta soma fafutukar ganin APC ta ba Osinbanjo tikitin tsaya mata takarar shugabancin kasar nan a zaben 2023.

‘Yan tsageran da ke tilasta wa jama’a zama a gida a jihohin Inyamurai,  na ci gaba da kai hari ofisohin ‘yan sanda,  da ofisoshin hukunar zabe,  da makarantu da yara ke rubuta jarabawar WAEC da sauransu

Jama’ar jihar Kano na ci gaba da kokawa a kan yadda ‘yan sanen waya da kwacenta suka cika Kano ba masaka tsinke,  har suna kashe mutane wajen kwace musu waya.

Gwamna Tambuwal na jihar Sakkwato ya nemi Gwamnatin Tarayya ta katse hanyoyin sadarwa ta waya a kananan hukumomi 14 na jihar don bullo wa matsalar tsaro a jihar ta bayan gida

Gwamnan jihar Legas Babajide,  ya sa hannu a dokar hana kiwon sake a jihar

LARABA 14 Ga Safar (22/09/21)

Daga watan Janairu na shekarar 2022 za a kara wa talakan Nijeriya kudin zama a duhu.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tura wa Majalisar Dokoki ta Kasa sabuwar dokar bangaren man fetur PIA a takaice don yi mata gyaran fuska da kwaskwarima.

  1. A Newyork/Niyok ta kasar Amurka inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke halartar taron Majalisar Dinkin Duniya, ya gana da Okonjo-Iweala shugabar hukumar hada-hadar kasuwanci ta duniya WTO a takaice.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabbin wakilai na hukumar hukumar EFCC mai yaki da laifuffuka na tattalin arziki da kudade.

Wadanda ke neman sarautar Kwantagora su 46 sun nuna rashin amincewarsu da wanda aka zaba.

Gwamnatin Jihar Kano ta haramta kallon fina-finai na kidinafin,  da ma’amala da miyagun kwayoyi.

Hukumomin sojan Nijeriya,  sun ankarar a game da yadda ISWAP mai nasaba sa kungiyar Boko Haram ke daukar jama’a aikinta na ta’adanci.

Majalisar Dattawa ta tura wa kwamitinta mai kula da al’amuran ciyo/ciwo bashi na kasashen waje da na cikin gida,  sabuwar bukatar da shugaban kasa Buhari ya gabatar,  ta sake ciyo wani bashin na Dala Biliyan Hudu da kusan rabi.

Wani rahoto na musamman da BBC ta yi a kan aikin wutar lantarki na Mambila,  ya bankado badakalar da aka kwashe shekaru ana yi da sunan aikin.

ALHAMIS 15 Ga Safar (23/09/21)

Jiya Laraba Majalisar Zartaswa ta Kasar nan FEC a takaice, ta gudanar da taron da ta saba yi duk Laraba,  wannan karon karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbanjo.  Da yake shi Shugaban Kasa Buhari yana can Amurka yana halartar taron Majalisar Dinkin Duniya. Taron na jiya ya yunkura a kan aikin Dam na Bagwai,  da masana’antar yin gas da majinyata kan shaka,  da sauran ayyuka a bangaren ilimi da na lafiya da ruwa da sauransu.

Majalisar Dattawa ta amince da wani tsari na matsakaicin lokaci na raya kasa na shekarar 2022-2024 (Medium Term Edpenditure Strategy Paper 2022-2024) MTEF a takaice.

Nijeriya ta yunkura, don karbo wata Fam ta Ingila,  Miliyan Dari Biyu da aka sata daga kasar nan aka je aka boye a Amurka.

Hukumar EFCC da ke yaki da laifuffuka na kudade da tattalin arziki ta zargi wani kamfani na Nijeriya da laifin damfarar Nijeriya bangaren kudaden tallafi

Gwamnati ta karbe wa tsohon gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed gida da ke Ilori a jihar Kwara.

Gwamna Zulum na jihar Barno, ya dakatar da ilahirin mahukunta kwalejin Ramat Foliteknik na tsawon wata shida sakamakon wata ziyarar – ba-zatta da ya kai makarantar ya tarar da ba daidai ba

 

Exit mobile version