Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC na ƙasa, Hon. Yekini Nabena, ya gargaɗi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya daina rura wutar gaba tsakanin yankin Arewa da Shugaba Bola Tinubu ko wani ɗan kudu gabanin zaɓen 2027.
Nabena ya bayyana cewa duk wani irin ƙoƙari da Kwankwaso ke yi na tayar da hankali ta hanyar amfani da ƙabilanci, ko addini ko kuma yanki domin bijirewa mulkin ɗan kudu ba zai yi tasiri ba. Ya ce dole ne ƴan kudu su yi shekaru takwas a shugabancin kuma ba za a sassauta ba don hakan shi ne tabbatar da adalci.
- Kula Da Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi
- Tinubu Na Yi Wa Arewa Manyan Ayyuka – Martanin Fadar Shugaban Ƙasa Ga Kwankwaso
Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP a 2023, ya zargi gwamnatin tarayya da nuna son kai wajen rabon arzikin ƙasa, yana mai cewa kudu na cin gajiya rabon fiye da Arewa. Ya ƙara da cewa hanyoyin mota a Arewa suna cikin yanayi mara kyau fiye da na Kudu.
Sai dai a martaninsa, Nabena ya ce Kwankwaso na ƙoƙarin hure wa al’ummar Arewa kunne ne domin gurgunta damar shugabancin ƴan kudu su kammala wa’adin shekaru takwas. Ya bayyana hakan a matsayin dabarar siyasa da ba za ta yi aiki ba, kasancewar mutane yanzu sun gane irin waɗannan shirye-shirye.
Nabena, wanda ya fito daga jihar Bayelsa, ya ƙalubalanci Kwankwaso da ya zagaya jihohin Kudu maso Kudu domin gwada hanyoyin da ke yankin da na Arewa. Ya ce: “Me ya sa ake kuka da rashin ci gaba a Arewa bayan shekara takwas da yankin ke rike da mulki?
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp