Matsalar karancin abinci a Nijeriya, na kara ci gaba da ta’azzara kamar yadda wasu manoma a kasar suka bayyana; inda suka ce, ana ci gaba da samun raguwar amfanin gona, sakamakon matsalar afkuwar iftila’in ambaliyar ruwan sama da sauyin yanayi da kalubalen rashin tsaro da kuma faduwar darajar Naira.
Haka zalika, shashen samar da abinci na Gwamnatin Kasar Amurka (USDA), ya yi hasashen cewa; za a samu raguwar noman Shinkafa, Gero, Rogo, Masara da kuma Waken Soya a wannan shekara 2024 a Nijeriya.
- Masu Masana’antu Na Kasar Sin Sun Raba Fasahohinsu A Majalisar Dinkin Duniya
- An Samu Sabuwar Damar Kyautata Hulda Tsakanin Sin Da Hungary
Koda-yake, wasu alkaluma sun bayyana cewa; Nijeriya ta kasance kan gaba a fadin duniya, wajen noma amfanin gonan da suka hada da Masara da Rogo.
Wasu jami’ai, a Ma’aikatar Aikin Noma ta Tarayya ta shaida wa LEADERSHIP cewa, ta samu madafar bayani kan matsayin amfanin da ake nomawa a kasar nan.
Har ila yau, duk da samun karin yawan manoma da aka yi a fadin wannan kasa, wasu manyan amfanin gonar za su fuskanci matsala; sakamakon faduwar darajar Naira, wanda hakan zai jawo raguwar noma a shekarar 2024.
Sai dai a 2022, alkaluma sun nuna cewa; an samu karin masu yin noma da kashi 119.9, duk da dimbin kalubalen da manoman kasar ke fuskanta.
Kididdiga ta baya-bayan nan, ciki har da wadda aka samo daga (USDA), sun yi hasashen cewa; an samu ruguwar noman Shinkafa a Nijeriya da tan miliyan 5.355 daga 2022 zuwa 2023 tare kuma da kara samun raguwar noman nata da tan miliyan 5.229 daga 2023 zuwa 20 24.
Haka zalika, an samu raguwar noman Masara da tan miliyan 12.75 a shekarar 2021, wadda ta kai kashi 8 cikin 100; sai kuma kara samun raguwar noman nata da tan miliyan 11 daga 2024 zuwa 2025.
Kazalika, an kuma samun raguwar noman Dawa da tan miliyan 6.742 daga 2022 zuwa 20 23, inda kuma za a kara samun raguwar noman Dawar da tan miliyan 6, 700 daga 2023 zuwa 2024.
Sashen samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya (FAO), ya yi hasashen cewa, ‘yan Nijeriya sama da miliyan 31.5; za su fuskanci karancin abinci daga watan Yuni zuwa na Agustan 2024.
Wani rahoto da Hukumar Samar da Abinci ta ‘Cadre Harmonise’ ta fitar ya nuna cewa, a watan Maris da ya gabata; Nijeriya ta fuskanci babban kalubalen rashin tsaro, wanda hakan ya jawo tsaiko wajen aiwatar noma.
Bugu da kari, a yayin da ake shirin fara yin noma gadan-gadan a wannan damina ta bana, an yi hasashen za a samu koma-baya ta fannin noma kwarai da gaske, musamman duba da yadda kalubalen rashin tsaro ke neman gagarar Kundila.
Shugaban Kungiyar Manoma ta Kasa (AFAN), Arc. Kabir Ibrahim; a hirarsa da LEADERSHIP, ya bayyana wasu daga cikin kalubalen da fannin aikin na noma a wannan kasa ke ci gaba da fuskanta, kamar kalubalen rashin tsaro, rashin samun kayan aikin noma na zamani, ambaliyar ruwan sama da kuma tsadar kudin da ake biyan leburorin da suke aiki.
Haka zalika, a Jihar Kwara noman Shinkafa, Masara, Gyada, Doya, Dawa, Wake da sauran amfanin gona ya yi matukar raguwa a lokacin noman rani da na damina daga shekarar 2022 zuwa 2023, inda wasu manoma a jihar suka sheda wa jaridar LEADERSHIP cewa, hakan ya faru ne sakamakon rashin samun dauki daga gwamnatin tarayya da kuma ta jihar.
Haka nan, a Jihar Biniwe noman Gero, Wake, Masara, Rogo, Gyada, Dawa da kuma Doya ya yi matukar raguwa a shekarar 2022, musamman saboda harin da wasu Fulani suka kai wa yankunan da ake yin noman, kazalika ambaliyar ruwan sama da kuma hare-haren ‘yan bindiga, wanda ya tarwatsa dimbin manoma daga matsugunansu.
Har wa yau, wasu manoma a Jihar Filato; kalubalen samun hare-haren ‘yan bindiga, musamman wanda aka kai a ranar 24 ga watan Disambar 2023, a Kananan Hukumomin Mangu da Bokkos; ya jawo wa manoma tabka asara.
A Jihar Bayelsa kuwa, matsalar kwarar danyen mai; ita ce babbar matsalar da manoma da gonakinsu ke fuskanta, musamman manoman Shinkafa.
Sai dai, wani manomin Shinkafa a yankin Akassa na Karamar Hukumar Brass a jihar, Mista Inatimi Peter Odio ya sheda wa LEADERSHIP Hausa cewa, matsalar kwarar danyen mai ya ragu; sakamakon kokarin da jami’an tsaron sintiri na Tantita suka yi a shekarar 2022, wanda hakan ya bai wa manoma damar noman Shinkafa.
Haka labarin ma yake a Jihar Neja, inda noman Doya da na Masara ya ragu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a kan manoma, domin kuwa har a yanzu wasu gonaki a yankunan Shiroro, Munya, Rafi, Mariga, Rijau da kuma wasu sassan Karamar Hukumar Paikoro da aka noma wadannan amfanin gona ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, wanda hakan ya tilasta wa manoma a wadannan gurare yin watsi da noman tare da yin kaura daga yankunan nasu, inda a yanzu suke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira a jihar.
Haka zalika, mai yiwuwa lamarin ba zai sauya akalar noman bana ba, duda da yadda maharan ke ci gaba da kai hare-hare kauyuka da dama na jihar.
Wannan batu haka yake a Jihar Osun ma, duba da yadda yawan Fulani Makiyaya ke yin kuste a gonakin manoma tare da satar amfanin gona, sannan kuma da yadda jihar ta fuskanci matsalar yin noma a kakar noma biyu.
Haka nan a Jihar Abiya, inda aka fara samun koma bayan a bangaren noma tun daga shekarar 2022, inda aka danganta matsalar kan amfani da kayan noma na gargajiya tare da rashin samar da ingantaccen Irin noma da tsadar kayan aikin noman da rashin samun goyon baya daga wurin gwamnatin jihar da rashin samar da rumbunan zamani na adana amfanin da aka noma da rashin samar da tituna don jigilar amfanin gonar da sace amfanin gonar da kuma hare-haren Fulani Makiyaya da sauran makamantansu.
A Jihar Ekiti kuwa, wani manomi Mista Olajide Olagunju ya ce, a watan Yunin 2022, noman Masara, Rogo da Doya ya yi matukar raguwa a jihar, sakamakon wasu matsaloli da suka hada da cututtukan da ke harbin amfanin gona da rashin samar da rumbuna na zamani wadanda za a adana amfanin gonar da aka noma, rashin samun takin zamani, gazawar samun rancen kudi daga bankuna, rashin samun saukar ruwa sama da wuri da sauransu.
A Jihar Sokoto kuma, shekaru biyu da suka gabata; noman Shinkafa, Gero, Masara, Rogo, Gyada, Doya da kuma Dawa ya yi matukar raguwa, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a wasu yankunan jihar.
Har ila yau, ita ma Jihar Kaduna ba ta tsira daga wannan matsala ba, domin kuwa wasu daga cikin manoman jihar sun danganta hakan da karuwar hare-haren ‘yan bindiga a wasu yankuna na jihar da kuma karancin kudi da wasu manoma ke fuskanta na kara noman Masara da Gero, domin ci da kuma sayarwa.
Wani manomin Masara; Gideon Cyprian, ya sheda wa LEADERSHIP Hausa cewa, hare-haren ‘yan bindiga ya yi matukar jawo koma-baya ga aikin noma a 2022, inda ya ce; a shekarar baya, ya girbe buhu takwas na Masara a wani kauye da ke jihar, amma sakamakon wannan hare-hare na ‘yan bindiga, yanzu ba ya iya zuwa gonar da ya karbi haya a wannan kauye, don gudanar da wannan aiki na noma.