Babban turken rarraba hasken wutar lantarkin Nijeriya ya fadi da safiyar yau Laraba, lamarin da ya jefa miliyoyin yan Nijeriya cikin duhu.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, turken ya fadi ne da misalin ƙarfe 11 na safe.
- Al’ummomi 44 Sun Yi Zanga-zangar Rashin Samun Wutar Lantarki Na Tsawon Shekara Daya A Kwara
- Zanga-zanga: Ku Kawo Ƙarshen Rashin Wutar Lantarki Da Ta Addabi Jihohi- Gwamnatin Kaduna
Kamfanin rarraba wutar lantarki na babban birnin tarayya Abuja, AEDC ne ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na X.
Kamar yadda kamfanin ya tabbatar, tuni aiki ya yi nisa wajen ganin an dawo da wutar.
Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekararnan ta 2025 da turken wutar ya fadi. A shekarar da ta gabata ta 2024 sau 12 turken yana faduwa, lamarin da ya janyo cece-kuce a faɗin ƙasarnan, inda wasu suke ganin akwai gazawar gwamnati, ya yin da wasu suke ganin wata makarkashiya ce wasu suke shirya domin kawai su samu kuɗi.