An Karrama Tsofaffin ‘Yan Wasa Da Masu Horaswa A Kaduna

Daga Shehu Abdullahi        

Kimanin tsoffin’yan wasan ƙwallon kafa,masu horaswa da masu tallafawa Harkan wasanni talatin a Kaduna aka karrama a filin wasa na YELWA da ke Telebishin a Kaduna alokacin da aka kara tsakanin kungiyar ƙwallon kafan Narayi da sabo.

Karramawar ta biyo bayan irin gudunmawar da suka bayar ko suke kan bayarwa a lokacin da wasun su suke raye

Waɗanda suka samu kyautar sun haɗa da marigayi Saleh Lato,tshohon mai horas da kungiyar ƙwallon kafa ta kaduna united, Sai marigayi tajudeen Olaiya tshohon Ɗan wasan kungiyar ƙwallon kafan D I C /Ranchers bees da marigayi Mohammed Perez tshohon mai horas da masu tsaron gidan kungiyar Remo stars ta jihar Ogun.

Sauran  sun haɗa da Ishaya Jatau,stephen Musa,Emmanuel Babayaro,Abdullahi Hayman,

Gamalial musa wanda duk sun bugawa ƙasar nan ƙwallo.

Har ila yau akwai coach fire,Coach Ade Nagogo Alhaji zakari ya’u da sauran su.

bukin wanda shi da ya dauki nauyin gasar,janar mohammed Sani Saleh ya dauki,ya gayeto manyan baki da suka haɗa da Hon. Sabo Babayaro, Hon.shehu Adamu tshohon komishinan matasa da wasanni na jihar,Alhaji Kasim Abdullahi sheriff,shugaban hukumar ƙwallon kafa ta jihar Kaduna, Hajiya Ladi Yahuza,tshohuwar shugaban riko ta chukun Alhaji Sani Abdullahi Walin Kakuri da sauran su.

A jawabin sa Janar Sani Saleh mai murabus ya yabawa waɗanda suka karbi kyautan,Sai ya yi kira ga sauran ‘yan wasa da su yi koyi da irin kokari da tarihi da ‘yan ƙwallon suka kafa.

Ɗaya daga cikin abin da ya jawo hankalin ‘yan kallo shi ne da janar Saleh ya bada kyaututtukan  wa wasu daga cikin matan  mamatan. An tsshi wasa tsakanin sabo da Narayi babu ci.

Exit mobile version