Kasafin 2020: Sanatoci Sun Kori Dan Aiken Fashola

A jiya Talata ne a ka bayar da rahoton cewa, kwamitin dorar da cigaban muradun karni (SDG) a majalisar dattawa sun ki sauraron Abubakar Aliyu, wanda shi ne karamin ministan ayyuka da gidaje.

Kwamitin na SDG ya bukaci Minista Babatunde Fashola ya zo gabansu da kansa ne, domin ya yi musu bayani ne kan tanadi kasafin kudi na 2020, amma sai ya turo mataimakinsa, wanda Majalisar Dattawan ba ta gamsu da hakan ba.

Shugabar wannan kwamiti, Aisha Dahiru Ahmed Binani, ta tubure a kan cewa dole sai Tunde Fashola ya hallara a gabansu da kansa, domin ya yi masu bayanin abubuwan da su ka shige mu su duhu.

Fashola ya tura Abubakar Aliyu ne domin ya kare kasafin ma’aikatar na shekara mai zuwa a gaban majalisar. Bayan hallarar karamin Minista da kimanin karfe 12:00, sai a ka juya ma sa baya.

 ‘Yan kwamitin sun nuna cewa babu abin da za su karba daga hannun Abubakar Aliyu domin babban Ministan su ke son gani a karan-kansa kamar yadda su ka rika ganawa da shi a baya. Sanata Tai Solarin, wanda ya na cikin ‘yan wannan kwamiti na SDG, ya koka da yadda Ministan ayyuka zai saba wa umarnin Buhari, ya yi tafiya ketare a daidai lokacin da a ke aikin kasafin kudi.

Malam Abubakar Aliyu ya yi kokarin yi wa sanatocin bayani cewa mai gidansa, Babatunde Fashola, ya bar Nijeriya ne bayan ya samu izinin Shugaban Kasa, amma ba su amince da haka ba.

Sanata Binini ta nuna fushinta ga yadda Ministan zai bar Nijeriya bayan an sanar da shi game da zaman.

A nan a ka yi ta jiran Raji Fashola har karfe 2:00 na rana, amma bai samu hallara ba.

Exit mobile version