Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa ɓangaren noma zai samu kaso 6.21 cikin 100 na kasafin Kuɗin shekarar 2024 da gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya gabatar a gaban zauren Majalisar dokokin jihar Katsina.
Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Katsina, Alhaji Bello Kagara ya bayyana haka ga manema labarai a Katsina.
- Gwamna Abba Yusuf Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnati
- Za Mu Samar Da Wutar Lantarki MW60 Ko Sola MW50 A Kowace Jiha -Gwamnonin Arewa Maso-Gabas
Kwamishinan ya ce, gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya tabbatar da kasafin kudin shekarar 2024 na Naira biliyan 454,308,862,113.96 amma ɓangaren ya samu naira biliyan 20, 513,909,753.71 inda haka ke nuna ya samu kaso 6.21%.
Haka kuma ya ƙara da cewa akwai manyan ayyuka da ake sa ran zasu lakume biliyoyin nairori a cikin kasafin shekarar 2024 da suka haɗa da ɓangaren Ruwan Sha da Ilimi da Kiwon lafiya da Ayyuka da Muhalli sai kuma noma.
” Bangaren ruwan sha ana sa ran zai lakume kimanin naira biliyan 67,161,802,447.39 inda yake wakilcin kaso 20.35% sai kuma ɓangaren ilimi da zai lakume naira biliyan 66,422,889,400.21 shima yana wakilcin kaso 20.13%” inji shi
Sauran ɓangarori sun haɗa da ma’aikatar ayyuka inda za a kashe kimanin naira biliyan 53,484,733,251.59 bisa wakilcin kaso 16.20% cikin ɗari, sai harkar kiwon lafiya ana sa ran zata kuɗi wuri na gugar wuri har naira biliyan 38,326, 421,172.23 cikin ɗari inda ta samu wakilcin kaso 11.43%.
Alhaji Bello Kagara ya cigaba da bayanin cewa ɓangaren muhalli zai samo naira biliyan 37,700,909,753.24 kaso 11.43% cikin ɗari wanda jumlar kuɗin suka kasance Naira biliyan 282,607,873,235.37
Tunda farko da yake jawabin sa Kwamishinan ya ce kasafin Kuɗin wannan shekarar na 2024 ya ɗararwa na bara da kimanin biliyan 153,675,604,150.96 daidai da kaso 51.11%
Kazalika Alhaji Bello Kagara ya ce wannan kasafin kudi na shekarar 2024 mai taken ‘Gina Gobe’ za a aiwatar da shi da waɗannan hanyoyin kuɗaɗen shiga.
A cewar Kwamishinan ana sa ran samun kuɗaɗen shiga daga hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta jihar Katsina da ma’aikatu da hukumomin gwamnati inda ake sa ran samun kimanin naira biliyan 25,826,650,462.67 sai kuma kuɗaɗen da wasu hukumomin gwamnati za su samar da suka kai kimanin naira biliyan 14,173,349,537.33
Sai kuma ya kara da cewa akwai kuɗaɗen da ake sa ran samu daga ɓangaren rabon arzikin ƙasa kimanin naira biliyan 148,061,977,186.28 da sauran ɓangarori na kuɗaɗen shiga.
Wannan kasafin kudi na shekarar 2024 bangaren ayyukan yau da kullum zai lashe kimanin naira biliyan 124,329,343,517.99 sai kuma manyan ayyuka za su kashi naira biliyan 329,979,518,595.97 jumla naira biliyan 454,308,862,113.96.