Kasar Aljeriya Ta Yi Nasarar Lashe Kofin Afirka

A jiya ce Kasar Aljeriya ta samu nasarar lashe gasar cin kofin kwallon kafa na Ksasshen Afirka wanda aka gudanar a Kasar Masar, inda ta doke takwararta ta Kasar Senegal da ci daya mai ban haushi a wasan karshe, wasan da aka buga shi a gaban dubun dubatar ‘yan kallo. An dai jefa wa Kasar Senegal kwallo a raga tun a zagayen farko na wasan inda har aka je hutun rabin lokaci aka dawo Kasar Senegal din ba su damar rama wannan kwallo daya tilo ba, duk da cewa suke taka muhimmiyar rawa a wasan tun daga farkon fara wasan har kusan karshen wasan.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ita Kasar Aljeriyan ta lashe wannan kofi. A shekarar 1990 shekarar da karbi bakuncin kasashen Afirka a matsayinta na mai masaukin baki ta samu damar lashe gasar. Kazalika Kasar Aljeriya ta fara buga wannan gasa tun a shekarar 1968 da aka gudanar a Kasar Habasha ko kuma Ethiopia, inda ta zo ta biyu. A 1980 da aka gudanar da gasar a Nijeirya ta zo ta biyu, a 1984 kuma ta kare a matsayin ta uku shekarar da aka gudanar da gasar a Kasar  Côte d’Iboire, haka nan ta sake zuwa a matsayin ta uku a kasar da gudanar da gasar  a 1988 da aka gudanar a Kasar Morocco. A takaice dai jimillar halartarta filin gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka sau 18, a wannan shekara kuma Allah ya sake ba ta nasarar lashe gasar a karo na biyu.

Exit mobile version