• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin: Amurka Ta Yi Matukar Kawo Cikas Ga Yarjejeniyar Da Aka Cimma A Tattaunawar Geneva

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
Amurka

A yau Litinin, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana cewa, Amurka ta yi matukar kawo cikas ga yarjejeniyar da aka cimma a tsakaninsu yayin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya a birnin Geneva, ta hanyar gabatar da matakan nuna wariya da dama a kan kasar ta Sin.

Mai magana da yawun ma’aikatar ya bayyana cewa, wadannan matakan sun hada da fitar da wasu tsare-tsare na dakile fitar da kayayyakin fasahar sadarwa na kirkirarriyar basira, watau AI Chip, da hana sayar da zayyanar manhajar fasahar ta Chip ga kasar Sin, da kuma sanar da soke takardar biza ga daliban kasar Sin.

  • Za A Samu Mamakon Ruwan Sama Da Hazo Daga Litinin Zuwa Laraba A Nijeriya
  • Babu Wanda Zai Iya Kora Ta Daga PDP —  Wike

Kazalika, jami’in ya ce, wadannan abubuwan da Amurka ta aikata sun yi matukar keta yarjejeniyar da aka cimma yayin wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugabannin kasashen biyu a ranar 17 ga watan Janairu, kuma sun yi mummunan cutar da muradu da danne hakkin kasar Sin.

Ya kara da cewa, Amurka ita kadai tsiga tsiyau ta rika tayar da husuma da sabbin tashe-tashen hankula na tattalin arziki da cinikayya ba sau daya ba, ba sau biyu ba, lamarin da ya kara ta’azzara rashin tabbas da tayar da zaune tsaye ta fuskar dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu.

Mai magana da yawun ma’aikatar ya kuma ce, “Maimakon ta yi wa kanta hisabi a kan abubuwan da take tafkawa, sai kuma Amurka ta zargi kasar Sin da karya yarjejeniyar, ikirarin da yake cike da yi wa gaskiya ungulu da kan zabo. Kuma tabbas, kasar Sin ta kafe kai da fata wajen yin fatali da wadannan zarge-zarge na rashin adalci.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Next Post
FERMA Na Bukatar N880bn Duk Shekara Domin Gyaran Tituna – Minista

FERMA Na Bukatar N880bn Duk Shekara Domin Gyaran Tituna – Minista

LABARAI MASU NASABA

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.