Kasar Sin na fatan dukkan bangarorin da rikicin Syria ya shafa za su sanya muhimman muradun al’ummar kasar Syria a gaba, da kuma samar da mafita a siyasance don gaggauta maido da kwanciyar hankali a kasar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana hakan yayin da take amsa tambayoyi masu alaka da halin da ake ciki a Syria.
Mao ta ce, kasar Sin na mai da hankali sosai kan halin da ake ciki a kasar Syria. Tana mai cewa, makomar Syria na hannun al’ummar Syria. Kana kasar Sin na fatan dukkan bangarorin da abin ya shafa za su samar da mafita ta hanyar siyasa don gaggauta dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali bisa ka’idar sanin ya kamata don muhimman muradun jama’ar kasar Syria na dogon lokaci. (Mohammed Yahaya)