• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Na Taimakawa Kasashen Afirka Bunkasa Sabon Karfin Samar Da Hajoji Da Hidimomi Masu Karko

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

A cikin rahoton aikin gwamnatin kasar Sin na shekarar 2024, an ce za a yi kokarin raya tsarin masana’antu na zamani a kasar, da gaggauta raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko. Kana shugaban kasar Sin Xi Jinping shi ma ya jaddada bukatar aiwatar da manufar bisa yanayin da mabambantan yankuna suke ciki. 

Dangane da hakan, wani shehun malami a tarayyar Najeriya mai suna Samson Ibion ya ce, ta la’akari da matsayin kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suka samar da mafi yawan gudunmowa ga karuwar tattalin arzikin duniya, manufar da kasar ta dauka ta raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, za ta amfani sauran kasashe masu tasowa. Lallai na yarda da ra’ayinsa.

  • Xi Ya Tattauna Harkokin Kasa Tare Da Wakilai Da Mambobin Manyan Taruka Biyu Na Kasar Sin
  • An Wallafa Littafi Na 1 Da Na 2 Na Littafin “Zababbun Kalamai Daga Jawaban Xi Jinping” Cikin Harshen Ingilishi

Alal misali, aikin samar da motoci masu yin amfani da makamashi mai tsabta dake tasowa cikin sauri a kasar Sin, shi ma ya samar da damammaki na samun ci gaba a kasashen Afirka.

A wajen taron makamashi na nahiyar Afirka na shekarar 2024, wanda ya gudana a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu a kwanan baya, fasahohin kera motoci masu aiki da wutar lantarki na kasar Sin da aka nuna a wajen taron sun janyo hankalin dimbin kwararru na kasashen Afirka. Aminene Merwe, ita ce darektar kamfanin Green Cab mai fasahohin kare muhalli na kasar Afirka ta Kudu. Ta ce motocin wutar lantarki na kasar Sin suna da makoma mai haske a kasuwannin kasar Afirka ta Kudu, saboda a cewarta, idan an kwatanta da motoci na sauran kasashe, “motocin kasar Sin suna da fifiko, ta fuskar yawan motocin da ake sayarwa, da farashi, da inganci, gami da karfin baturansu. ”

A lokaci guda, kamfanonin kasar Sin sun fara hadin gwiwa da takwarorinsu na kasar Habasha, don samar da motocin wutar lantarki a can. Kasancewar kasar Habasha ta samu isasshiyar wutar lantarki, ta hanyar samar da ita ta karfin ruwa, ya sa gwamnatin kasar ke sa ran ganin wata makoma mai haske game da aikin samar da motocin wutar lantarki a kasar, inda take taimakon raya bangaren ta hanyar samar da wasu manufofi na gatanci. A nasu bangare, kamfanonin kasar Sin sun samu yafuwar harajin kwastam na shigo da sassan mota da aka yi musu, ta hanyar kafa ma’aikatun hada sassan motoci a kasar Habasha. Lamarin da ya ba su damar rage kudin da ake kashewa wajen samar da motoci, da farashin motocin da ake samarwa, gami da raya masana’antu, da samar da karin guraben aikin yi a kasar.

LABARAI MASU NASABA

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

Ta wadannan misalai za mu iya ganin cewa, da farko, yayin da kasar Sin ke kokarin neman raya sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko, ita ma ta kai shi kasashen Afirka. Na biyu shi ne, ingancin kayayyakin Sin, da farashinsu, da fasahohin kasar, da tsarinta na zuba jari, dukkansu sun dace da ainihin yanayin da ake ciki a kasashen Afirka. Wannan ya kasance dabarar da ake dauka ta raya harkoki bisa yanayi da muhalli da ake ciki.

Bari mu dauki wani batu da ya shafi aikin sadarwa a matsayin misali. Kamfanin tantance yanayin kasuwannin kimiyya da fasaha na kasa da kasa Canalys, ya gabatar da wasu alkaluma a kwanan baya, wadanda suka nuna cewa, kamfanin samar da wayoyin salula na Transsion na kasar Sin, ya sayar da wayoyin salula har miliyan 34 da dubu 500 a kasashen Afirka a shekarar 2023, adadin da ya kai rabin wayoyin da aka sayar da su a nahiyar. Ta haka, kamfanin ya zama wanda ya sayar da mafi yawan wayoyin salula a nahiyar Afirka.

To, ko me ya sa wayoyin salula na kamfanin ke samun karbuwa a kasuwannin Afirka? Dalilin shi ne yadda kamfanin ke mai da cikakken hankali kan bukatu na mutanen nahiyar Afirka. Wayoyin salula na kamfanin, suna da fifiko, wato da farko ya fi biyan bukatun al’umma bakaken fata wajen daukar hotuna. Na biyu, ana iya sanya katuna na SIM da yawa a cikin wayar salula guda. Na uku, wayoyin salular suna kunshe da tsarin sarrafawa na harsunan Afirka. Yayin da na hudu, suke da batura masu karfi da dorewa. Na biyar, a cikin wayoyin salular akwai APP mai kunshe da dimbin wakokin kasashen Afirka. Na shida shi ne, akwai wayoyin salula iri-iri da za a iya zaba, kana dukkansu na da inganci da araha. To, duk wadannan halaye ne na musamman da suka dace da bukatun mutanen kasashen Afirka, da muhallin wuraren zaman su, wadanda suka sa wayoyin salula kirar kamfanin ke samun karbuwa a kasashen Afirka.

A sa’i daya kuma, wannan kamfani na kasar Sin ya kafa cibiyoyin kirkire-kirkire, da masana’antu, da sassa masu kula da sayarwa, da samar da hidimomi, a kasashen Najeriya, da Kenya, da Habasha, da dai sauransu, ta yadda aka kai fasahar sadarwa ta zamani a nahiyar Afirka, da samar da guraben aikin yi da damammaki na raya kai ga matasan nahiyar.

To, duk wadannan misalai ne na yadda kasar Sin take kokarin raya masana’antun zamani da sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko a kasashen Afirka, bisa yanayin da kasashen suke ciki.

Wani shehun malami mai suna Robert Gituru, wanda ke jami’ar fasahohin aikin noma ta Jomo Kenyatta ta kasar Kenya, yayin da yake hira da manema labaru a kwanakin baya, ya ce, bisa matsayinta na kasa dake kan hanyar tasowa, kasar Sin ta fi sauran sassa fahimtar kalubalolin da kasashen Afirka suke fuskanta, kana tana da dabarun warware matsaloli da za su biya bukatun kasashen Afirka.

A ganina, wannan shi ne dalilin da ya sa fasahohin kasar Sin, da manufofinta ke samun karbuwa, gami da samar da hakikanin gudunmowa a kasashen Afirka. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 4, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan
Ra'ayi Riga

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 4, 2025
A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?
Ra'ayi Riga

A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?

November 2, 2025
Next Post
Sheikh Gumi Ga Tinubu: Ka Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga, Kada Ka Zama Irin Buhari

Sheikh Gumi Ga Tinubu: Ka Yi Sulhu Da 'Yan Bindiga, Kada Ka Zama Irin Buhari

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.