Kasar Sin Ta Bayyana Matsayinta Game Da Shawarar Da WHO Ta Gabatar Na Gudanar Da Aikin Binciken Gano Asalin Kwayar Cutar COVID-19 Zagaye Na Biyu A Kasar

Daga CRI Hausa

A jiya ne ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya kira taron manema labarai, inda ya gabatar da batun aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19.

Yayin taron, masana da dama sun bayyana cewa, babu wani abu da ya sulale a dakin bincike na Wuhan, kuma abu ne mai wahala, cutar ta bulla daga dakin gwajin. Haka kuma kasar Sin, ba zata taba yarda da batun gudanar da aikin binciken gano asalin cutar a karo na biyu da hukumar lafiya ta duniyar ta gabatar ba.

A jawabinsa, mataimakin darektan hukumar lafiya ta kasar Sin Zeng Yixin, ya bayyana cewa, yana mamaki jin yadda wasu mutane suke ikirarin wai, kwayar cutar dake haddasa COVID-19 (SARS-coV-2) ta bulla ne daga cibiyar binciken cututtuka ta Wuhan (WIV).

Yana mai cewa, wannan ikirari, abu ne da hankali ba zai taba dauka ba, kana ya sabawa mataki na kimiya.

Shi ma darektan dakin binciken kwayoyin halitta na kasa a cibiyar binciken na Wuhan, Yuan Zhiming, ya bayyana cewa, kasancewar dakin binciken a matsayin P4, ba a taba samun sulalewar wasu sinadarai a dakin gwajinsa, tun lokacin da ya fara aiki a shekarar 2018 zuwa yanzu.

A makon da ya gabata ne, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ba da shawarar sake gudanar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar a kasar Sin. Wuraren da za a sake gudanar da wannan bincike a wannan karo, sun hada da kasuwar sayar da albarkatun ruwa da kuma dakin binciken kwayoyin cututtuka dukkansu a birnin Wuhan.

Da yake mayar da martani kan wannan batu Zeng Yixin, ya bayana cewa, tunanin da ake yi game da wai yadda kasar Sin ta keta ka’idojin tafiyar da dakin bincike ne, ya haddasa bullar cutar” yana daya daga cikin muhimman sassan da binciken zai mayar da hankali akai.

Wannan a cewarsa, batu ne da ko kadan hankali ba zai dauka ba, kana bai dace da tsari na kimiyya ba”.

A don haka, kasar Sin ba za ta taba amincewa da irin wannan shiri na aikin binciken gano asalin kwayar cutar ta COVID-19 ba. (Ibrahim)

Exit mobile version