Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Zhang Xiaogang, ya gargadi Amurka game da yunkurin amfani da yankin Taiwan domin cimma bukatun siyasa, ta hanyar kokarin mallakawa yankin na Taiwan na kasar Sin makamai, yana mai cewa hakan na iya haifarwa Amurka mummunan sakamako.
Zhang Xiaogang, ya yi tsokacin ne yayin da yake mayar da martani game tambayar da manema labarai suka yi masa, dangane da sabon kudurin dokar tsaro da majalisar dokokin Amurka ta amincewa, wadda a cikinta aka tanadi samar da kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan daya, domin karfafa abun da Amurkan ta kira da “karfafa hadin gwiwar ayyukan soji” tsakanin Amurka da yankin na Taiwan.
Zhang, ya ce sassan kudurin dokar marasa dacewa da moriyar Sin sun zamo tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin, da keta hurumin ’yancin mulkin kai, da tsaro da ci gaban moriyar kasar Sin, za su kuma gurgunta zaman lafiya da daidaito tsakanin sassan kasa da kasa.
Kakakin ya kuma jaddada matukar adawa, da tanade-tanaden dokar, yana mai cewa, batun Taiwan shi ne jan layi na farko da ba za a iya tsallakewa ba a dangantakar Sin da Amurka.
Daga nan sai ya yi kira ga Amurka, da ta mutunta cikakkiyar manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da kuma sanarwa uku na hadin gwiwa da Sin da Amurka suka amincewa, ta yadda za ta cika alkawarin da ta dauka na kin goyon bayan duk wani yunkuri na neman ’yancin kan Taiwan, kana Amurka ta kaucewa mika sakwanni na kuskure ga ’yan aware masu rajin neman ’yancin kan yankin na Taiwan, ko shiga duk wata cudanyar ayyukan soji da yankin Taiwan na kasar Sin. (Saminu Alhassan)