A yau Alhamis, kasar Sin ta harba kumbon Shenzhou-18 mai dauke da ‘yan sama jannati 3 zuwa tashar sararin samaniya ta Tiangong, domin gudanar da aiki na tsawon watanni 6.
An harba kumbon ne ta hanyar amfani da rokar Long March-2F, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin.
- Yawan Kayayyakin Da Sin Ta Samar Ya Wuce Misali Ko Damuwar Amurka Ta Wuce Kima?
- An Kaddamar Da Bikin Nune-nunen Shirye-shiryen Bidiyo Da Sinima Na Kasar Sin A Kasar Serbia
A cewar hukumar kula da ayyukan kumbo mai dauke da ‘yan sama jannati ta kasar Sin (CMSA), ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-18 sun hada da Ye Guangfu da Li Cong da Li Guangsu, karkashin jagorancin Ye Guangfu.
Wannan shi ne karo na biyu da Ye Guangfu ya tafi sararin samaniya, inda a baya ya kasance daya daga cikin ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-13, daga watan Oktoban shekarar 2021 zuwa watan Afrilun shekarar 2022, yayin da wannan ne karo na farko ga Li Cong da Li Guangsu. (Fa’iza Mustapha)