Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai gana da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G20.
Lokacin da aka tambaye shi ko taron zai kunshi batutuwan da suka shafi yankin Taiwan da jihar Xinjiang, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau cewa, batutuwan yankin Taiwan da Xinjiang, dukkan su manyan batutuwa ne dake shafar babbar moriyar kasar Sin.
Zhao Lijian ya ce, batun Taiwan batu ne mai muhimmanci a dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka. Don haka, ya kamata bangaren Amurka ya martaba sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da kasashen Sin da Amurka suka cimma, da daina yin karya da keta manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, da daina nuna goyon bayan neman ‘yancin kai na Taiwan, da kiyaye tushen siyasa na dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka tare da aiwatar da su a zahiri.
Yayin da yake karin haske kan batun da ya shafi jihar Xinjiang kuwa, Zhao Lijian ya jaddada cewa, batun wai “aiki na tilas a jihar Xinjiang” wata babbar karya ce da Amurka ta kitsa, don neman bata sunan kasar Sin da ma dakushe ci gabanta.
Saboda haka ya ce, muna kira ga bangaren Amurka, da ya daina kitsa karairayi game da tilastawa ‘yan kwadago, da dakatar da aiwatar da “dokar hana aikin tilas ta Uygur”, da daukar managartan matakai don samar da kyakkyawan yanayi na hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban, maimakon haifar da sabbin cikas.(Ibrahim)