Don samar da karin kwararru, da inganta kwarewar aiki na ma’aikata, hukumomin kasar Sin guda 7, ciki har da ma’aikatar kula da harkar samar da guraben aikin yi da tabbatar da ingancin rayuwar jama’a, sun sanar a kwanan baya da cewa, za a kaddamar da wani shiri na horar da kwararru a kasar tsakanin shekarar 2024 da ta 2026, inda ake neman samar da kwararrun da suke iya jagorantar wani bangaren aiki fiye da dubu 15, da kwararru masu fasahohin sana’o’i kimanin miliyan 5.
An ce za a dora muhimmanci kan horar da kwararrun da suke iya jagorantar ayyuka masu alaka da sabbin nau’ikan masana’antu, da bangaren samar da hidimomi na zamani, da dai sauransu, ta yadda za a biya bukatun kasar na raya wasu manyan tsare-tsare, da gudanar da wasu manyan ayyuka na gina kasa, a karkashin manufar kasar ta raya kasa ta hanyar samar da dimbin kwararrun da ake bukata.
An kuma kara da cewa, za a samar da shirye-shiryen horar da kwararru, don inganta kwarewarsu ta fuskar aiki, da aiwatar da shirin da aka tsara, gami da kirkiro sabbin fasahohi, ta yadda za a samu damar raya masana’antu, da aiwatar da manyan tsare-tsaren kasar. (Bello Wang)