Kasar Sin za ta ci gaba da daukar kwararan matakai don tabbatar da daidaiton dadaidaiton tsarin masana’antu da na samar da kayayyaki a duniya ba tare da cikas ba.
Firaministan kasar Sin Li Qiang ne ya bayyana hakan yau Litinin a lokacin da yake halartar taron bita tare da wakilan kamfanoni da kungiyoyin da za su halarci bikin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na biyu da ke tafe a birnin Beijing, babban birnin kasar Sin. (Yahaya)