Ministan kudi na kasar Sin Liu Kun, ya bayyana a yayin taron jami’an kudi na kungiyar G20 da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga watan Yuli cewa, kasar Sin ta kudirin aniyar ba da gudummawar dalar Amurka miliyan 50 ga asusun shiga tsakani na harkokin kudi, wanda bankin duniya ya amince da shi wajen kandagarkin annoba .
Liu ya ce, ya kamata kasashe mambobin kungiyar G20 su ci gaba da kiyaye matsayin kungiyar a matsayin babban taron dandalin hadin gwiwar tattalin arziki na kasa da kasa, da daidaita matakan rigakafi da kandagarkin annoba da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa, da kiyaye tsaro da daidaiton masana’antu da tsarin samar da kayayyaki a duniya, da kuma hana faruwar mummunar barna daga gyare-gyaren manufofi da wasu kasashe suka aiwatar.
Liu ya ce, kasar Sin tana goyon bayan hanyoyin hada-hadar kudi na kungiyar G20, don gudanar da mu’amala da musayar ra’ayi kan manufofin sauyin yanayi, da kiyaye ka’idojin aiki na bai daya amma banbanta.
Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin tana son yin aiki tare da dukkan bangarori, don cimma matsaya bai daya wajen zuba jari mai dorewa a fannin samar da kayayyakin more rayuwa masu inganci wadanda jama’a suke bukata. (Ibrahim Yaya)