kasar Sin ta fitar da wata takardar sanarwa, kan kara hada-hadar kasuwanci ta yanar gizo a yankunan karkarar kasar, da tsarin isar da sakonni da kayayyaki ga jama’a, a wani mataki na kyautata alaka da samar da abinci a tsakanin birane da kauyuka.
Wata sanarwar hadin gwiwa da ma’aikatar kasuwanci tare da wasu hukumomin gwamnati bakwai suka fitar, ta bayyana cewa, Kasar Sin, za ta inganta cibiyoyin rarraba kayayyaki a matakin gundumomi da gina shiyoyin gwaji, don bunkasa kasuwancin yanar gizo na yankunan karkara da ayyukan isar da sakonni da kayayyaki.
Sanarwar ta ce, kasar Sin na son kara saukaka jigilar kayayyakin amfanin gona daga kauyuka zuwa birane, da kayayyakin masarufi daga birane zuwa kauyuka.
Haka kuma, za a dauki matakan karfafawa kananan hukumomi gwiwa, don inganta ababen more rayuwa a yankunan karkara, da yayata gina na’urorin jigilar kayan dake bukatar sanyi, don adana kayayyakin amfanin gona, da karfafa sassa masu rauni a fannin jigilar kayayyaki dake bukatar sanyi a wuraren da ake noman irin wadannan kayayyaki.(Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp