Shugaban kasar Sin, Xi Jinping a taron BRI da ke wakana a birnin kasar, Beijing ya jaddada aniyar kasar na kammala layin dogo na Abuja zuwa Kano da na Fatakwal zuwa Maiduguri.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaba Tinubu Stanley Nkwocha, shugaban kasar Sin ya bayyana aniyarsa na kammala aiyukan ne yayin da ya amsa bukatun da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar, wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilta a taron da kasashen biyu suka yi da kasar Sin.
- Tabbatar Da Daidaito Da Cin Moriyar Juna Suna Cikin Babban Ruhin Shawarar BRI
- Tinubu Ya Kaddamar Da Shirin Raba Naira Tiriliyan N1.25 Ga Magidanta Miliyan 15
Idan dai za a iya tunawa, tun bayan kaddamar da aiyukan, har yanzu kasar Sin ba ta fitar da kudaden gudanar da manyan ayyukan layin dogo guda biyu a Nijeriya ba da ta yi alkawari, saboda aiyuka da shirye-shirye da suka yi wa kasar Katutu.
Kasar Sin ta amince a baya za ta samar da kashi 85 cikin 100 na kudaden gina layin dogon daga Abuja zuwa Kano da Fatakwal-Maiduguri, yayin da Nijeriya za ta samar da kashi 15 cikin 100, tuni Nijeriya ta biya na bangarenta tun farkon fara aikin.
Kamfanin Gine-gine na China (CCECC) shi ke da alhakin kammala kwangilar aikin.
Shugaban kasar Sin ya yi alkawarin kara zuba jari a fannin samar da wutar lantarki da bangaren kimiyya a Nijeriya, ya kuma yi kira da a kare ‘yan kasar Sin da ke aiki a Nijeriya, yana mai cewa, zai tabbatar da cewa, dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da Sin ta yi karfi fiye da yadda ta ke a baya.