Gwamnatin lardin Hainan ta kaddamar da aikin kaurar da mutane a shekarar 2019, da nufin kare muhallin halittu da mazauna kauyuka daga kara fadawa cikin kangin talauci. Za a kammala kashi na farko na aikin da ya kunshi kafatanin al’ummar kauyen Gaofeng, a karshen bana.
Fu Yongzheng, mazaunin kauyen Gaofeng na garin Nankai dake gundumar Baisha mai cin gashin kanta, ya ce barin yankin tsaunikan ba abu ne mai sauki a wajensa ba kasancewar ya dade yana rayuwa a wurin, sai dai kuma ya zaku matuka. Za su fara sabuwar rayuwa a yankin da aka gina da nufin tsugunar da mutane daga wurin da zai zama yankin yawon shakatawa na gandun dajin Hainan dake lardin tsibirin Hainan.
Fu daya ne daga cikin mutane 498 na iyalai 118 da suka zamo rukuni na farko da aka kaurar daga yankin shakatawa na gandun daji na farko da ake ginawa a kasar Sin.
Kaurar da mutanen wani bangare ne na shirin kawar da talauci da biyan bukatunsu na samun rayuwa mai inganci a wajen tsaunika.
Kafin fitar da shi daga jerin masu fama da talauci a shekarar 2017, kauyen Gaofeng daya ne daga cikin mafi fama da talauci a lardin. Daga cikin iyalai 118, 101 na fama da fatara mai tsanani, inda suka dogara kadai kan noman itatuwan roba.
Nisan kauyen da kuma rashin kyan hanyar sufuri sun kara talauta yankin. Yadda yake cikin tsaunika, sannan yake da nisan kilomita 62 daga gari mafi kusa, ya sanya kauyen nisanta da sauran yankuna.
An ba kowanne iyali a Gaofeng gida mai hawa 2 dake da fadin muraba’in mita 115, wanda gwamnati ta bada kudin ginawa.
Gwamnatin gundumar Baisha, ta kuma samar da gonar noman laimar kwadi da hadin gwiwar wani kamfani dake kusa da yankin.
Baya ga samar da gonar, har ma da yuan 180,000 (dala 27,522) da za a rika ba mazauna duk shekara.
Har ila yau, an kuma gayyaci wani kamfanin sarrafa ganyen shayi domin ya kafa cibiyarsa a wurin, da nufin samar da aikin yi. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Kyautata Alakar Sin Da Amurka Zai Taimakawa Gwamnatin Biden Wajen Shawo Kan Manyan Kalubale
Kamar yadda muka sani, shugaban Amurka na 46 Joe Biden,...