Idris Aliyu Daudawa" />

Kasashe 194 Suka Tsawatar Kan Kasuwancin Tabar Sigari Ta Bayan Fage

A halin da ake ciki yanzu kasashen duniya wadanda suke mambobin majalisar dinkin duniya 194 (WHO), daga karshe dai, sun amince da yadda da za a sa wasu su bar shan taba sigari, ko kuma su rage.

Amincewar kamar yadda majalisar dinkin duniya ta (WHO) ta bayyana cewar ita tafiyar an faro ne tun shekarau shida da suka wuce, lokacin da aka fara ita maganar yiyuwar yin hakan.

Hukumar ta kara bayyana cewar shi taron wanda aka yi akan yadda za a kafa doka wadda zata kula abin sharudda dangane da illar da shan  taba sigari, yake kawowa, wanda wata kungiya ce mai suna Framework Conbectiion on Tabacco Control, a takaice dai taron kungiyar da take sa ido dangane da illar taba sigari, da kuma kokarin hana shanta. An kuma dain amince da wannan al’amarin ne, a daular Turawa ta UK. An samu dukkan abubuwan da ake so dangane da saboda yadda za  a kawo karshen harakar kasuwancin kayayyakin da suka shafi sigari, za kuma a fara amfani da ita dokar ne nan da kwanaki 90.

‘’Wannan ba wata maganar kunbiyta kunbiya sako ne da ga kasashen kasa da kasa saboda su kawo karshen wannan sana’a wadda take bata matsala ga rayuwar al’umma, ta hanyar cinikayyar taba da wasu nau’ointa, kamar dai yadda yadda Darekta Janar na Hukumar lafiya ta duniya Tedros Ghebreyessus, ya bayyana cewar wannan ‘’ Shine mataki na farko wanda za a kao karshen ita wannan cinikayya ta kayayyakin sigari a duniya baki daya’’.

Hukiumar lafiya ta duniya ta bayyana cewar shi matakin da aka fara dauka ba karamin ci gaba bane, a tarihin kokarin da ake yin a kawo karshen fataucin taba sigari, wanda abin ya shafi kaso uku, wadanda suka hada da yadda ake, yadda za a samar da amfani da doka, samar da yadda za ayi amfani da ita dokar.

Ba ada da bayan haka akwai ma maganar yadda ake rarraba ita tabar, wanda za ayi magani lasisi, sa ido sosai , da kuma yadda za a rika rubuta bayanann halin da ake ciki, yadda za agano da da akwai wani kokari na yinnabinda bai dace ba, wannan shi zai ba gwamnati sanin halin da ake ciki, a ko wanne lokaci, wanda ya hada da ga Kmafanin da ake yin tabar zuwa wurin ada ake kaia saboda sayarwa.

Shi dai matakin ya samar da hadin kan kasa da kasa cikakke wanda ya hada da musanyar bayanai wadanda suka shafi fasaha, da kuma doka wadda ta shafi hadin kan kasashe, da kuma taimako wanda ya shafi harkar mulki da al’amarin da ya shafi  mayar da wani abu ko kuma wani ya tafi zuwa wata kasa .

An dai amince da hakan tun shekarar 2012 a taron kungiyar na biyar, wanda hakan ya kasance dole ne saboda harkokin da ake yin a kasuwanci taba sigari, da kuma wasu kayayyakinta, wanda kum  ba karamar barzana bace akan kula da lafiyar al’umma.

Kamar dai yadda Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana yadda kasuwancin taba sigari, ta hanyar da bata dace ba,  tana samar da hanya wadda ake yi da bata dace ba, maimakon a samar da wahala wajen fataucinta.

Wannan abinn ya samar da matsala rasa kudaden shiga ga aljihun gwamnati, duk kuma  a lokaci daya al’amarin yana samar da hanya ta aikata laifuka.

Babban abin da ya sa aka dauki matakin domin kawo karshen dukkanin abubuwan da basu dace ba, da suka danganci hanyoyin da basu dace ba, na yadda ake fataucin ita tabar, dawasu nau’oin kayayyakin ta, kamar dai yadda dokar Article 15 na Hukumar lafiya ta duniya, wadda ta kun shi, hanyoyin da suka shafi yadda za a kawo karshen yadda ake kasuwancin da bai dace ba.

 

Exit mobile version