Nijeriya ta samar da wani kudiri da aka amince da shi a makon da ya gabata wanda ya yi kira ga kasashen da suke dauke mata likitoci su rika biyan diyyar kudaden da gwamnati ta kashe wajen ilmantar da su.
Ministan Lafiya, Dakta Muhammed Ali Pate, ya bayyana haka a shirin BBC Hausa na tattaunawa a tsakanin shugabanni da al’umma kan matsalolin da ke addabar ‘yan kasa mai taken “A Fada A Cika” da aka gudanar ranar Laraba a Abuja, wanda aka gayyaci LEADERSHIP Hausa.
- Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Bukace Lauyoyin Su Mayar Da Kwafin Takardun Shari’ar
- Gwamna Nasir Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Naira Biliyan 250 Ga Majalisar Dokokin Kebbi
Yayin da aka tambaye shi wace hanya za a bi domin magance tserewar da likitoci ke yawan yi daga kasar nan zuwa wasu kasashen waje, ministan ya ce akwai matsaloli da dama da suke addabar fannin lafiya da ya kamata su likitocin su yi masu duba na tsanaki tare da nuna kishin ƙasa.
“Abin da ya dace su likitocin su fara dubawa shi ne, na farko dai ko da mutum ba a makarantar gwamnati ya yi karatu ba to babu makawa gwamnati ta taka rawa a al’amarin da ya shafi iliminsa ta wata fuskar, don haka kamata ya yi su fara duba kishin kasar kafin su yi tunanin barin kasar saboda rashin albashi. Nijeriya kasarmu ce kuma babu wanda zai zo ya gyara mana in ba mu ba.
“Na biyu kuma, su tuna cewa akwa jami’an da suka sadaukar da rayuwarsu domin kare rayukan ‘yan Nijeriya kuma ake biyan su kudin da bai kai nasu yawa ba, misalin sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro, kuma aikinsu ya fi na likitocin wahala, ka ga wannan ba wani abu ne ba illa kishin kasa, domin albashin nasu ba wani yawa ne da shi ba, wannan kishin kasa ne. Don haka ya kamata kasashen da suke dauke mana likitoci su fara biyan mu kudaden da muka kashe wajen ba su ilimi domin mu samu sukunin maye gurbin wadancan da suka dauke mana. Mun cimma matsaya kan haka a makon da ya gabata kuma za mu gabatar musu da bukatar hakan,” in ji shi.
Ya ce cututtuka sun karu kuma kudaden da gwamnati ke kashewa wajen kula da lafiyar jama’a ma sun karu duk da ba su kai yadda ake so ba, “kana saboda kashi 80 cikin 100 na kayan da ake harhada magunguna shigo da su ake daga waje, ya sa magungunan sun yi tsada kuma yanzu kowa ya san yadda farashin Dala yake, don haka dole sai gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da kuma jama’a sun taimaka wa gwamnatin tarayya.
“A kokarin da muke yi na inganta aikace-aikacen kula da lafiya, a tsakanin wata uku da rantsar da mu a matsayin ministroci, mun yi bincike kan wasu mutum 2,500 domin ganin yadda za mu raga yawan matsalolin da ake fuskanta na kiwon lafiya. Sakamakon binciken, yanzu haka mun sha damarar ganin an samar da asibito na sha-ka-tafi a kowace mazaba da ke fadin kasar nan. Wannan zai kara inganta kiwon lafiya a matakin farko.
“Kuma abin da ya kamata mutane su sani shi ne, gwamnatin tarayya ita kadai ke ba da kaso 70 na kudaden gudanar da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko. Duk da haka wannan bai isa, a kullum Dala 10 ake kashewa ga lafiyar kowane dan Nijeriya, wannan ya yi karanci kwarai da gaske, domin Ingila Fam 5,000 take kashewa, Amurka Dala 14,000. To amma duk wannan ba za mu iya hada kanmu da sub a saboda yanayin tattalin arzikinmu, sai dai duk da haka za mu kara kokari kuma su ma jihohi su kara yawan abin da suke bayarwa ga kiwon lafiya,” in ji shi.
Da yake bayani a kan inshorar lafiya kuwa, Dakta Pate ya bayyana cewa, tun a 1974 Nijeriya ta fara shirin Inshorar lafiya. Bincike ya nuna kaso 10 ne daga cikin ‘yan Nijeriya suke da Inshorar lafiya, don haka a yanzu shugaban kasa ya rattaba hannu a kan tilas a shigar da kowane dan Nijeriya cikin Inshorar lafiya. Sannan akwai gidauniya ta tallafa wa marasa lafiya da ba su da galihu wanda a yanzu haka akwai mutum miliyan 1.7 da suke cin gajiya. Ka ga wannan bai wadatar ba”
Har ila yau, ministan ya shawarci ‘Yan Nijeriya su rika zuwa asibitoci ana duba lafiyarsu domin idan aka gano cututtuka irin su na Koda, Siga, AIDS da hawan jini, da sauransu da wuri, ana iya fara magani tun kafin abin ya ta’azzara.
Ministan ya kuma bayyana kokarin da suke yi na sarrafa magunguna a cikin gida maimakon kasashen waje, inda ya nunar da cewa akwai kusan kamfanoni 150 da za a zauna da su domin cimma wannan kudiri.