An Kashe Masu Zanga-zanga 30 A Kenya

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’ Adam ta Human Rights Watch da kuma Amnesty International, sun ce ‘yan sandan ƙasar Kenya sun hallaka a ƙalla mutane 33, yayin ƙoƙarin murƙushe masu zanga-zanga. Zanga-zangar ta ɓarke ne tun bayan sanar da nasarar shugaba mai ci Uhuru Kenyatta, wanda daga bisani kotun ƙolin ƙasar ta soke.

Sai dai janyewar jagoran ‘yan adawa Raila Odinga daga sake sabon zaɓen a wannan wata, ya sake rura wutar zanga-zangar. Aƙalla dai mutum 30 ake zargin ‘yan sanda suka kashe a yayin gudanar da zanga-zanga da ‘yan adawa suka yi a birnin Nairobi na ƙasar Kenya.

A wani sabon rahoton da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta fitar ta ce, ‘yan sandan ƙasar ‘’suna da hannu dumu-dumu’’. Har ila yau, akwai waɗansu rahotanni da ba a tabbatar ba, wadanda suke cewa ‘yan sandan sun kashe waɗansu mutum 17 a birnin.

Suna zargin ‘yan sandan da tayar da zaune tsaye ta amfani da ƙarfin da ya wuce kima a yankunan da ake tunani cewa ana tashin hankali. Ƙungiyar ta ce ‘yan sandan sun yi amfani da karfin da ya wuce kima ne a wuraren da ake zaton rikicin.

A makon da ya gabata ne jagoran ‘yan adawar ƙasar, Raila Odinga, ya ce ba zai shiga zaɓen shugaban ƙasa da za’a sake yi a cikin wannan watan. Saboda ba shi da imanin cewa za a yi  adalci a zaben, a cewarsa.

 

Exit mobile version