Duk da irin makudan kudade da ake ware wa bangaren ilimi a Nijeriya, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kashi 31 na ‘yan Nijeriaya ba su iya karatu da rubutu ba.
Karamin ministan ilimi, Rt Honourable Goodluck Opiah, shi ya bayyana hakan a wurin taron ma’aikatu kan ranar jahilai ta duniya ta 2022 tare da ganin an kawar da lamarin cikin sauki.
Ya ce a yanzu haka alkaluman 2022 sun nuna cewa akwai kashi 31 na jahilai a kasar nan, inda ya ce adadin ya ragu da na shekarar 2015 da aka samu kashi 38.
Ministan ya kara da cewa wannan rana da Majalisar Dinkin Duniya ta ware na tantance adadin marasa ilimi ya bayar da damar bunkasa harkokin ilimi tare da inganta fannin a ko’ina a fadin duniya.