Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar sama da kashi 50 na magungunan da ake sayarwa a kasashen Afirka ta Yamma marasa inganci ne, abin da ya sa sukan bijire wa cututtuka da kuma sanya mutane rashin amincewa da tsarin kula da lafiyar da ake amfani da su.
Ofishin majalisar da ke kula da magunguna, ya ce tsakanin watan Janairun shekarar 2017 zuwa Disambar shekarar 2021 akalla tan 605 na irin wadannan magunguna marasa inganci aka kwace a yankin daga masu safarar su.
- Jirgin Sama Kirar Kasar Sin Samfurin C919 Ya Tashi A Karon Farko Cikin Sabuwar Shekarar Zomo
- Masani: Sin Za Ta Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasa Ci Gaban Duniya A Shekarar 2023
Majalisar ta ce a kowace shekara ana kashe kudin da ya kai kusan Dala miliyan 45 wajen kula da lafiyar jama’ar da suka yi amfani da irin wadannan magunguna marasa inganci a matsayin maganin cutar zazzabin cizon sauro, yayin da ake samun mutane dubu 267 da ke mutuwa kowace shekara saboda kwankwadar magungunan.
Bayan magungunan marasa inganci, majalisar ta yi kuma gargadi a kan yadda ake amfani da wasu magunguna ta hanyoyin da ba su kamata ba, abin da ke haifar da bijirewar wadanda ake amfani da su wajen kare kai daga cutar zazzabi.
Francois Patuel, shugaban sashen bincike da kula da magungunan Majalisar, ya ce ba a iya sanya ido wajen ganin yadda ake amfani da magungunan da zarar sun bar kamfanonin da aka sarrafa su.
Rahotan wanda ya mayar da hankali a kan safarar magungunan ta barauniyar hanya ta kasashen Mauritania da Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma Chadi, ya ce ana karkata su ne daga Turai da China da kuma Indiya, yayin da suke bi ta gabar ruwan kasashe irin su Guinea da Ghana da Togo da Benin da kuma Nijeriya zuwa yankin Sahel baki daya.
Majalisar ta ce mutanen da suke amfana da safarar wadannan gurbatattun magunguna sun hada da ma’aikatan kamfanonin da ake sarrafa su da jami’an tsaro da kuma masu sayar da su a kan tituna.