Hukumar tsarawa da lura da jarabawar marantu masu koyar da harshen Larabci da ilimin addinin Musulunci ta kasa (NBAIS) ta saki sakamakon jarabawara watan Yuni zuwa Yulin 2022.
Hukumar ta ce kashi 78 cikin 100 na daliban da suka rubuta jarawa suka ci sakamako mai kyau.
- Ranar Malaman Kasar Sin: Menene Sirrin Ci Gaban Kasar Sin?
- Za Mu Iya Ciyar Da Kifayen Da Muke Kiwo Da Mushe?
Shugaban hukumar NBAIS, Farfesa Shafi’u Mohammad shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata da ta gabata a Kaduna a yayin kaddamar da sakamakon jarabawara ga manema labarai.
A cewarsa, dalibai dubu 45 sukayi rajistar jarabawar, amma guda dubu 33,977 ne suka rubuta jarabawar a jihohi 24 da babban birnin tarayya Abuja.
Farfesa Shafi’u ya tabbatar da cewa hukumarsa za ta yi iya bakin kokarinta wajen wayar da kan wadansu makarantun gaba da sakandare da suke ganin cewa wadanda suka rubuta jarabawa a hukumar a bangaren kimiyya ba za su iya karatu a makarantar gaba da sakandare da sakamakon ba.
Sai dai ya tabbatar da cewa suna da bayanai da ke nuni da cewa dalibansu da suka rubuta jarabawa a hukumar sun shiga makarantu a cikin Nijeriya da ma wajenta da sakamakon kuma suna nuna kokari sosai a bangaren kimiyya.
Ya kara da cewa hukumar ba kawai ta takaita karatunta ga bangaren addinin Musulunci da harshen Arabiya ba ne kawai, har da sauran darussu daban-daban.
Farfesa Shafi’u ya jinjina wa ma’aikatar ilimi ta tarayya bisa jagoranci Adamu Adamu saboda irin gudunduma da karfin gwiwar da take bai wa hukuma.