Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jagoranci taron majalisar tattalin arzikin ƙasa a Abuja, a daidai lokacin da al’ummar ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki.
Hukumar ta NEC da ke ba shugaban ƙasa shawara kan tattalin arziki, ta ƙunshi gwamnonin jihohi, da gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), da kuma ministan ƙudi. Wannan taron yana da mahimmanci musamman, musamman duba da yadda ake tattaunawa game da yadda za a samo mafita a batun mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
- Kashim Shettima Ya Ƙaddamar Da Shirin ASSEP A Bauchi
- Gwamnatin Kano Za Ta Dauki Masu Gadi 17,600 Don Bai Wa Makarantun Jihar Tsaro
A farkon makon nan ne dai gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu zai ƙara tuntubar masu ruwa da tsaki kafin ya kammala yanke shawara kan sabon mafi ƙarancin albashi.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron na NEC da ke gudana yanzu haka akwai; gwamna Usman Ododo (Kogi), da Uba Sani (Kaduna), da Lawal Dauda (Zamfara), da Charles Soludo (Anambra), da Seyi Makinde (Oyo), da Lucky Ayedatiwa (Ondo).
Haka kuma a wurin taron akwai gwamnoni Abdullahi Sule (Nasarawa), da AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara), da Caleb Mutfwang (Plateau), da Hope Uzodimma (Imo), da Biodun Oyebanji (Ekiti), daa Muhammed Inuwa Yahaya (Gombe) da Peter Mbah (Enugu), da Francis Nwifuru (Ebonyi), da Dapo Abiodun (Ogun), da Umar Radda (Katsina), da Abba Yusuf (Kano), da Umar Namadi (Jigawa), da kuma Umar Bago (Niger).
Mataimakan gwamnonin da ke wakiltar jihohinsu sun haɗa da na Legas, da Ribas, Borno, da Adamawa, da kuma Yobe.