Wani jami’in hukumar kula da musayar kudaden waje ta kasar Sin, watau SAFE Li Bin ya bayyana cewa, kasuwancin shige da fice da zuba jarin kasar Sin ta wannan fuskar ya samu karin tagomashi a shekarar 2024.
Jami’in wanda shi ne mataimakin shugaban hukumar ta SAFE, ya yi bayanin haka ne a wani taron manema labarai da ofishin yada labarai na gwamnatin kasar Sin ya kira a yau Talata.
- Ana Hasashen Yawan Tafiye-Tafiye Za Su Kai Biliyan 9 Yayin Bikin Bazara Na Kasar Sin
- Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Murar Tsuntsaye A Kano
Ya kara da cewa, harkokin karba da biyan kudi da aka yi ba ta hanyar banki ba ciki har da na kamfanoni da na daidaikun ‘yan kasuwa, sun karu da kashi 14.6 a mizanin shekara-shekara zuwa dala tiriliyan 14.3 a bara. Inda hakan ya zama mafi kololuwa da aka taba samu.
Kazalika, Li ya ce an ci gaba da samun daidaito a bangaren biyan kudi, kana hada-hadar asusan ajiya na musayar kudaden waje sun tafi yadda ake so ba tare da nukusani ba da fiye da dala tiriliyan 3.2, yana mai karawa da cewa, farashin musayar kudin kasar Sin RMB shi ma ya tafi daidai-wa-daida ta yadda ba a samu tasgaro ba a bangarensa. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)