Ga dukkan alamu yunkurin da jam’iyyun adawa ke yi na yin kawance domin yakar jam’iyya mai Mulki ta APC ya shiga garari, yayin da wasu manyan jam’iyyun adawa suka nesanta kansu da lamarin.
A ranar Alhamis 7 ga Disambar 2023, wasu rahotanni sun yi nuni da cewa akwai wasu jam’iyyun adawa su 7 da suke kokarin yin kawancen siyasa domin fatattakar jam’iyyar APC daga kan maragar mulkin Nijeriya.
Gamayyar jam’iyyun sun kunshi PDP da ADC da SDP da PAM da NNPP da YPP da kuma ZLP.
Taron hadin kan sun yi ne da nufin yakar jam’iyya mai mulki ta APC, wanda rahotanni ya nuna cewa shugabannin jam’iyyun ne suka yi wannan taron a babban hedikwatan jam’iyyar SDP da ke Abuja.
Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam ya ce jam’iyyun sun gaji matuka kan yadda yanayin kasar nan yake a birkice, babu wani abu da ke tafiya daidai, musamman yadda ake samun rudani a shari’u da aka yi na gwamnoni kanar a jihohin Zamfara da Nasarawa da Kano da Filato.
Jami’iyyun adawa dai sun yi rashin nasara a kotuna a wadannan jihohin bayan da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ayyanasu a matsayin wadanda suka yi nasara.
Bayanai dai na nuna cewa babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta sami wakilci a taron, inda mai rikon mukamin sakataren jam’iyyar na kasa, Senonji Koshedo ya wakilci mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Umar Damagum.
A cewar shugabannin jam’iyyun adawar dai, babban dalilin wannan hadin kan shi ne a tabbatar da ingancin dimokuradiyya a Nijeriya ta hanayar samun jam’iyyar adawa mai karfin gaske da za ta iya tunkarar jam’iyya mai mulki.
Amma kuma wasu bayanai na nuna cewa kawancen da aka yi bai kai ga yin maja ba, ma’ana jam’iyyun siyasar za su kasance a matsayinsu na jam’iyyu masu zaman kansu ko da za su yi aiki tare don kawar da APC.
Ko da yake wasu na ganin cewa wannan kawance nasu ba mai yiwuwa ba ne don kowa manufarsa daban. Sanin kowa ne sai hali ya zo daya ake abota.
Haka kuma wasu bayanan na nuna cewa wasu wakilan jam’iyyun da suka halarci taron sun je ne a karin kansu ba da yawun jam’iyyunsu ba.
Duk da yake mai rikon sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Koshoedo ya halarci taron ya kuma nuna goyon bayansa a taron, amma jam’iyyar PDP ta nesanta kanta da hadin gwiwar. Sakataren watsa labaran PDP, Debo Ologunagba, ya musanta shiga tattaunawar yin kawance da jam’iyyun adawan guda shida.
Ita ma a nata bangaren, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar NNPP ya nesanta kansa da shiga tattaunawar kawance da wasu jam’iyyun adawa. Jam’iyyar NNPP ta kasa ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Abba Ali, ya fitar a birnin tarayya Abuja. Ya ce NNPP ba ta daga cikin mambobin gamayyar jam’iyyun da suka cure wuri daya domin yin kawance.
Sanarwar ta ce, “An jawo hankalin shugabancin jam’iyya kan wasu rahotannin da jaridu suka wallafa cewa an kafa gamayyar jam’iyyu kuma ta kunshi NNPP da wasu jam’iyyun siyasa.”
“Muna mai farin cikin sanar da cewa babu wani abu makamancin haka. Rahoton wanda ya watsu ranar Jumu’a, 8 ga watan Satumba, 2023 ya nuna cewa NNPP, PDP da wasu jam’iyyu sun yi kawance.”
Ali ya kara da cewa tun bayan zaben 2023, babu wani mamban NNPP da ya zauna da wata jam’iyya ko tawaga ko daidaiku da nufin tattaunawar kawance.
Jam’iyyar LP sun barranta kansu da shiga wannan hadaka kamar yadda mai magana da yawun jam’iyyar, Obiora Ifoh ya bayyana. Ya ce ba da su ba, don ba a kama hanyar hadin kai ba. ya ce idan za su yi hadaka za su duba tanaje-tanajen dokokin zabe da ya samar a kan hadaka.
Alamu dai na nuna cewa gamayyar jam’iyyun adawa ba su tsara ainihin yadda za a yi hadakar ba, duk da yake sakataren hadakar jam’iyyun, Willy Ezugwu ya ce hadakarsu na jam’iyyu masu rajista a Nijeriya ne, don haka ba suna karkashin wani ba ne da za su amsa sunansa.
Abun da kowa zai duba shi ne, hannu daya ba ya daukan jinka, kuma idan ana neman samun nasara a kowani abu dole ne a hadu waje guda don a sami nasarar, kamar abun da ya faru a shekarar 2014 inda jam’iyyun adawa suka hadu suka kafa jam’iyyar APC wanda ta sami nasara a zaben shekarar 2015.