Sanata Suleiman AbdulRahman Kawu Sumaila, mai wakiltar yankin Kano ta Kudu – wanda ita ce Sanatoriya mafi girma a Nijeriya da ƙananan hukumomi 16, mazabu 171 da fiye da mutane miliyan 5 – ya bayyana godiya ga Gwamnatin Jihar Kano bisa matsayinta na goyon bayan ƙirƙiro sabuwar jiha da ƙarin ƙananan hukumomi a cikin jihar ta Kano.
Sanatan ya bayyana hakan a matsayin mataki na ci gaba da kuma amincewa da ƙudirin dokarsa da ke gaban Majalisar Dokoki ta ƙasa, wanda ke da burin inganta shugabanci da bunƙasa yankin.
- ‘Yansanda Sun Damke Mutum Shida Kan Kisan Da Aka Yi A Kasuwar Abuja
- Kawunan Shugabannin Arewa Sun Rabu Kan Siyasar 2027
A cikin wata sanarwa, Sanata Kawu Sumaila ya ce:
“Matsayar da Gwamnatin Kano ta ɗauka kwanan nan alama ce ta cewa muna tafiya akan hanyar ci gaba. Waɗanda ke adawa da ƙirƙiro Jihar Tiga abokan gaba ne ga ci gaban Kano ta Kudu da ma Kano gaba ɗaya. Mutanenmu sun cancanci wakilci nagari, da shugabanci na gari da kuma adalci wajen rabon albarkatu.”
Ya ƙara da cewa kafa Jihar Tiga zai bai wa jama’a damar samun sauƙin gudanar da harkokin gwamnati, ingantattun ayyuka, da kuma ƙarin damar tattalin arziƙi da cigaba.
Sanatan ya kuma buƙaci jama’ar Kano ta Kudu da Kano gaba daya da su haɗa kai:
“Yanzu lokaci ne da ya kamata mu haɗe da juna domin samun cigaba. Mu daina rarrabuwar kai, mu tsaya tsayin daka wajen ganin burinmu ya cika. Idan muka haɗa kai, babu abin da zai hana mu samun ci gaba da makoma mai kyau.“
A ƙarshe, ya roki shugabannin al’umma da sauran ƴan ƙasa da su goyi bayan wannan yunƙuri tare da ƙin amincewa da duk wata dabara ta rarrabuwa da za ta hana nasarar da ake fata daga ƙirƙiro Jihar Tiga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp