Shugabannin Arewa daga kungiyoyin dattawan Arewa na NEF da ta ACF, sun dauki matsaya daban-daban kan wanda za a zaba a matsayin shugaban a 2027.
Yayin da NEF ta ce za ta dauki tsaya kan zaben shugaban kasa na 2027 nan da watanni shida, ACF ta ce ba za ta bayyana goyon baya ga kowane dan takara ba.
- ‘Yan Sama Jannati 3 Na Kumbon Shenzhou-20 Na Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniyar Sin Cikin Nasara
- Tinubu Ya Tabbatar Da Aniyar Gwamnatinsa Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Tsohon mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin siyasa a ofishin mataimakin shugaban kasa kuma jigo a kungiyar dattawan Arewa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa a cikin watanni shida masu zuwa, Arewa za ta fito ta sanar da matsayinta kan batun.
Ya kara da cewa kungiyar dattawan Arewa ba za ta lamunci cin zarafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.
Sai dai da take magana da LEADERSHIP, ACF ta bayyana cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani dan takarar shugaban kasa a bainar jama’a a zaben 2027 ba.
Da yake magana ta wayar tarho a ranar Lahadi, sakataren yada labarai na ACF na kasa, Farfesa T.A. Muhammad Baba, wanda aka nemi ya yi tsokaci kan kalaman Baba-Ahmed, ya ce a matsayinsa na dattijo, Baba-Ahmed yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa.
Mai magana da yawun ACF, duk da haka, kungiyar za ta bincika dukkan batutuwan tare da gabatar da su ga masu jefa kuri’a don su iya yin zabi mai kyau a 2027.
“Dakta Baba-Ahmed yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa. Bai dade da ya bar cikin gwamnati ba, kuma duk abin da ya ce hakkinsa ne. Kun san muna gab da zabukan 2027, kuma yawancin irin wadannan ra’ayoyin mutane da kungiyoyi za su bayyana a yayin da zabuka ke gabatowa. Muna sa ran ganin karin irin wannan sharhi. Ko yake, ACF ba kungiya ce ta siyasa ba. Ba ma nuna bangaranci.
“Yayin da zabe ke gabatowa, za mu iya nazarin batutuwa ne kawai mu gabatar da su ga masu jefa kuri’a don su yanke shawarar wanda za su zaba. Ba za mu bayyana goyon baya ga duk wani dan takarar jam’iyyar siyasa da zai tsaya takara a zaben shugaban kasa a 2027 ba. Za mu ci gaba da kasancewa a matsayin kungiyar kare muradun al’ummar Arewa,” in ji ACF.
A halin da ake ciki, wata kungiya mai suna ‘Arewa Think Tank’ (ATT), ta nuna goyon baya ga matsayin Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule cewa ya kamata Arewa ta yi aiki don sake zaben Bola Tinubu a 2027.
A kwanan nan ne Gwamna Sule ya bayyana cewa Arewa na bukatar hada kai don aiwatar da yunkurin Shugaba Tinubu ba.
A kan kashe-kashen da aka yi kwanan nan a jihohin Filato da Benuwai, Arewa Think Tank ta yi zargin cewa makiyan ‘yan siyasa suna yin duk mai yiwuwa, ciki har da shigar da kasashen waje, don kawo cikas ga gudanar da babban zabben 2027.
A cikin wata sanarwa da shugaban ATT, Muhammad Alhaji Yakubu ya fitar, ya ce kungiyar ta sha alwashin goyon bayan yin tazarcen Shugaba Tinubu, domin ya ci gaba da ayyukan da ya faro.
“Mun san cewa goyon bayan wa’adi na biyu na Shugaba Tinubu zai cika alkawarin da ya yi wa yankin Arewa tun gabanin babban zaben 2023.
“Mun amince kuma mun goyi bayan Gwamna Sule saboda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ta tsakiya, kuma mun san cewa ba a san Arewa da yin watsi da alkawuran da ta dauka ba.”
ATT ta bukaci shugabannin Arewa da su nesanta kansu daga wasu ‘yan siyasa da ke da niyyar rikitar da siyasar Nijeriya saboda sun kasa cimma burinsu.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta rufe kan iyakokin kasar nan tare da hana bakin haure shigowa Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp