A yau Alhamis ne wani rukunin kayayyakin agajin gaggawa da gwamnatin kasar Sin ta bayar ya isa birnin Vanuatu na Port Vila.
Kunshin kayayyakin agajin mai nauyin ton 35 ya hada da tantuna, gadaje masu nadewa, fitilun sola, abinci, ababen tsabtace ruwa da kayayyakin jinya.
Girgizar kasa mai karfin awo 7.3 ta afku a Port Vila a ranar 17 ga watan Disamba, inda ta kashe mutane a kalla 14, tare da raunata fiye da 200 tare da matukar lalata ababen more rayuwa na birnin. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya)