An bayyana cewa ba karamar nasara a ka samu ba a tafiyar hadaddiyar kungiyar masu kishin cigaban jihar Kano, wato Kano Concern Citizens Initiatibe (KCCI), domin yanzu al’ummar Kano; ’yan kasuwa, sarakuna, ’yan siyasa da malamai sun fara ganin nasara da fahimtar kungiyar.
Don haka wannan abin farin ciki ne ga dukkan al’ummar Kano; matasa, maza da mata, a ce an fara cimma inda wannan kungiya ta sa gaba a halin yanzu, wanda burinta shi ne kwato hakkin mutanen Kano a kowanne fanni da mataki da kuma hada kan jagororin al’umma a wannan zamani.
Wannan bayanin na kunshe ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban hadaddiyar kungiyar ta KCCI, Alhaji Bashir Othman Tofa, kuma daya daga cikin dattawan Kano kuma dan kasuwa kuma tsohun dan siyaya, wanda ya yi takarar shugabancin kasa a rusasshiyar jam’iyyar NRC a Jamhuriya ta Uku.
A cikin wannan takarda da a ka raba wa manema labarai ciki kuwa har da LEADERSHIP A YAU LAHADI, ta nemu dukkanin zababbun da a ka zaba a jihar Kano tun daga kan gwamna da ’yan majalissar dattawa da na wakilai da kuma ’yan majalisar jiha da su tabbatar sun hada kansu wajen kwato wa Kano ’yancinta da zai kawo ma ta cigaba, domin hakan shi ne siyasar cigaba, ba siyasar kyashi da hassada da kauyanci ba duk da kasancewa KCCI ta hada daukacin al’ummar Kano masu kishinta ba tare da ta karkata zuwa ga wata jam’iyya ba.
Don haka ta na bukatar hadin kai ne kurum tsakanin al’ummar Kano, don a samu cigaba ta kowanne fanni.
Haka kuma a cikin wannan takarda mai shafi uku shugaban na KCCI, Bashir Tofa, ya bayyana takaicinsa a kan karancin masu fitowa su yi rijistar zabe ta yadda ba sa wuce kashi 20%, wanda haka kuma za ka ga cewa mutane masu zuwa kada kuri’a da zaben shugabanni ba sa wuce kashi 12% a cikin 20% yayin da kashi takwas zuwa 10 an rarraba su ne ga sauran jam’iyyu, wanda kuma babban hatsari ne a ce mafi karancin al’umma su ne su ka zabi shugabanni, domin idan ka duba a tsarin kuri’a za ka ga cewa kashi 30% ba a yarda su yi kuri’a ba, saboda karancin shekaru. Kashi 70 ne kawai su ka cancanci yin kuri’a kuma su yi zabe.
Saboda haka akwai bukata da wajabcin duk lokacin da a ka zo yin kuri’a, inda duk wanda ya cancanta ya fito ya yi.,haka ma zabe dukkanin al’umma su fito su yi. Don haka ne akasarin mutane za su zabi shugabanni ba mafi karanci a cikin al’ummarsu.
Haka kuma Alhaji Tofa ya bayyana cewa wannan KCCI za ta cigaba da aiki dare da rana, don tabbatar da cewa an inganta shugabancin Kano da tsarin tattalin arzikin Kano ta hanyar dawo da ingancin kasuwancin Kano, noma da kiwo da kuma kyakykyawan tarihi da zamantakewa na da a ka gada iyaye da kakkanni tun shekaru aru-aru kyakykyawan misali ga rayuwar magabatanmu irinsu Malam Aminu Kano da Malam Yusufu Maitama Sule da Malam Inuwa Wada da sauransu, wadanda su ka yi matukar zarra tare da fice a fegensu.
Jami’ar Tarayya Ta Gusau Ta Musanta Labarin Harin ‘Yan Bindiga
Daga Hussaini Yero, Shugabannin Jami'ar gwamnatin Tarayya dake Gusau (FUG)...