Gwamnatin jihar Kebbi ta ƙarfafa shirinta na bunƙasa kiwo ta hanyar haɗin gwuiwa da ƙasar Brazil domin haɓaka sarrafa naman ta hanyar zamani a jihar.
Tawagar Brazil ta JBS SA Executives za ta isa Birnin Kebbi a ranar Litinin don duba hanyoyin zuba jari da haɗin gwuiwa a fannin kiwon dabbobi, sarrafa nama, da lafiyar dabbobi.
- Ra’ayin Matasa Kan Kungiyar ‘Yan Ta’adda Mai Suna Lakurawa Da Ta Fito A Kebbi
- Gwamnatin Kebbi Ta Dakile Yunkurin Lakurawa Na Satar Shanu
A cewar kwamishinan ma’aikatar lura da lafiyar kiwon dabbobin da kiwon kifi Mallam Kabir Usman Alaramma, a yayin ziyarar za a daidaita haɗin gwuiwa tsakanin jihar Kebbi da ƙasar Brazil. A laramma ya yi nuni da cewa, martabar jihar Kebbi a matsayin babbar cibiyar harkokin kiwon dabbobi a nahiyar Afrika na ƙara samun karɓuwa a duniya.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne ga manema Labarai a yayin wani taron manema Labarai da ya shirya a ofishin manema Labarai da ke Birnin Kebbl.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron manema labaran da aka gudanar a Birnin Kebbi akwai: Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi da kwamishinan tsare-tsare da raya birane Alhaji Hayatu Bawa.