Tarihi ba ya gushewa saboda kawai wasu sun kawar da kai daga gare shi. Kalaman baya bayan nan da ake ji daga wasu jagororin Japan, dangane da batun yankin Taiwan na kasar Sin abun damuwa ne. Kuma sun baiwa duniya mamaki kwarai da gaske, ganin cewa Japan a matsayinta na kasa wadda ta sha kaye a karshen yakin duniya na biyu, a yanzu wai ita ce ke kokarin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Abun lurar a nan shi ne a tarihi kafin Japan ta mamaye Taiwan, babu wata matsala tsakanin Sin da Japan, amma bayan mamayar, Japan ta kafa mummunan tarihin muzgunawa, da cutar da bil’adama, tare da haifar da rarrabuwar kawuna a shiyyar da take.
A cikin shekarar 1895 ne Japan ta kwace yankin Taiwan daga gwamnatin daular Qing ta lokacin, karkashin wata yarjejeniyar rashin adalci ta Shimonoseki. Bayan mamayar Japan, yankin na Taiwan ya fada matsanancin hali da tashe-tashen hankula, da kwashe albarkatun kasa, da kokarin kawar da al’adun al’ummun yankin. Don haka, wani bangare da tarihin Taiwan ba zai manta da shi ba, shi ne mugun raunin da Japan ta yiwa yankin Taiwan, da rashin adalcin da ta bari a tarihinsa.
A yayin yakin duniya na biyu, sama da al’ummun Taiwan 300,000 Japan ta tursasawa shiga ayyukan soji, kuma kusan 30,000 daga cikinsu sun rasu a kasashen ketare. Baya ga dubban matan Taiwan da dakarun Japan din suka tursasawa zama bayi da ake cin zarafinsu.
Dukkanin wadannan, ta’asa ce da tarihi ya kiyaye, wadanda har abada al’ummun duniya ba za su taba mantawa da su ba. Bayan da Japan ta mika wuy;a a karshen yakin duniya na biyu cikin shekarar 1945, bayan shafe shekaru 50 tana mulkin mallaka ga Taiwan, al’ummun yankin na Taiwan sun cika da murna da san barka. Wanda hakan ya zama shaidar kubutarsu daga mulkin danniya, da komawa cikin ’yan uwa dake sauran yankunan kasar Sin.
Bisa wadannan abubuwa da suka faru a tarihi, za mu gane cewa, duk yadda aka yi kokarin yiwa tarihi gyaran fuska, ba za a iya maye gurbin gaskiya da karya ba, kana ba za a iya binne adalci ba. Tarin laifukan da Japanawa ’yan mamaya suka aikata ga al’ummun Taiwan ba zai bace ba, ko a sauya shi ta hanyar amfani da wasu kalamai na farfaganda.
Abun da zai iya sassauta radadin ta’asar Japan shi ne yin karatun baya, da tuba na hakika, da gyara kura-kurai. Kazalika, ya zama wajibi Japan ta fuskanci gaskiyar tarihi, ta yi tunani, da kokarin biyan bashin tarihi, ta yadda za a kai ga warware dukkanin batutuwa masu nasaba da hakan. (Saminu Alhassan)














