Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya danganta yaduwar makamai tsakanin ’yan Nijeriya da kafa ƙungiyoyin tsaro na jihohi. A cewar Kwankwaso, matsalar ta nuna cewa gwamnatin tarayya tana fama da fuskantar gazawar dakile ta.
A wata sanarwa da ya wallafa a X ranar Litinin, Kwankwaso ya ce: “Abubuwan da ke faruwa a ƙasarmu kwanan nan sun cika ni da damuwa matuƙa game da halin da harkokin ƙasa ke ciki.” Ya bayyana cewa, yayin da ɗaukar matakin dakile rashin tsaro ya rataya ne a wuyan gwamnatin tarayya, ya kamata a yi hakan tare da haɗin gwuiwar gwamnatocin jihohi, da kananan hukumomi, da sauran masu ruwa da tsaki.
- Kwankwaso Ya Tarɓi Gwamna Abba Yusuf A Abuja Bayan Kyautar NEAPS
- APC Ba Ta Da Ƙarfin Da Za Ta Lashe Zaɓen 2027 Ba Tare Da Kwankwaso Ba – Dungurawa
Kwankwaso ya kuma soki amincewar da aka bai wa jihohi su kafa ƙungiyoyin tsaro na sa-kai, inda ya ce: “Duk da cewa manufar tana da kyau, wannan mataki ya haifar da yaduwar makamai kanana ba tare da kulawa ba a fadin ƙasa.” Ya ƙara da gargadin cewa wasu mutane suna amfani da wannan damar wajen kafa rundunoni nasu, abin da ke ƙara barazana ga zaman lafiya a ƙasa.
Tsohon Ministan Tsaron ya bayyana damuwarsa kan ƙara samun nuna bambanci bisa kabila da yanki, inda ake tsangwamar wasu mutane, da tsare su ba bisa ka’ida ba, ko kuma azabtar da su a wasu sassan ƙasar. Haka zalika, ya nuna yadda ƙara samun cin zarafi, da tsangwama da kuma maganganun ƙiyayya a kafafen sada zumunta ke ƙara ƙarfafa rigingimu na kabilanci da addini.
Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa ya ce waɗannan abubuwa na barazana ga haɗin kai da zaman lafiya. Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin dakile waɗannan halaye kafin su ƙara zama babbar barazana, tare da nuna cewa yaduwar makamai a yanzu abin takaici ne kuma ba abin da za a yarda da shi ba ne.














