Daga Mahdi M. Muhammad,
Bisa al’adarsa ta yin bukukuwa tare da dakarun Sojin saman Nijeriya (NAF), wadanda ke aiki a fagen-daga, Babban Hafsan sojojin sama (CAS), Air Marshal Sadikue Abubakar, ya shirya liyafar cin abincin rana don bikin ranar ‘Yuletide’ tare da jami’an sojin sama na ‘Air Task Force (ATF), bangaren tawagar ‘Operation LAFIYA DOLE’ (OPLD) a Maiduguri da Yola da kuma jami’an NAF da ke aiki a Katsina a karkashin hedikwatar tsaro (DHK) da ke karkashin tawagar ‘Operation HADARIN DAJI’ (OPHD).
Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka abcikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, inda yake cewa, liyafar cin abincin na Kirsimeti wanda aka yi a ranar, 25 ga Disamba, 2020, a wurare daban-daban, cikin bin ka’idojin cutar korona.
Daramola ya ci gaba da bayyana cewa, an yi wannan biki ne don yaba wa hazikan sojoji saboda irin kokari da sadaukarwa da suke yi a kullum yayin da ba su da lokacin jin dadin bikin tare da iyalansu da abokan arziki.
Da yake jawabi a lokacin liyafar cin abincin a Maiduguri, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, wanda Mataimakinsa, Hon. Umar Kadafur, ya wakilta a matsayin babban bako na musamman na girmamawa, babban Hafsan ya ce, irin wadannan masu taruwa suna taimakawa wajen karfafa dankon zumunci tare da samar da hanya ga NAF don yabawa da irin kokarin da dukkan jami’an da ke cikin ayyukan yakar tayar da kayar baya.
Babban Hafsan ya ci gaba da cewa, bikin Kirsimeti ya kasance biki ne na sadaukarwa, wanda jami’an NAF a matsayin kwararrun sojoji, ke iya kokarinsu don tabbatar da hadin kai a Nijeriya. A cikin kalmominsa ya ce, “Ba abu ne mai sauki ba iya kididdigar dimbin gudummawar da kuka bayar, wani bangare shi ne yin bikin kirsimeti a fagen-daga, duk a kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin kasarmu. Saboda haka, NAF tana tare da ku kamar yadda kuka gani a gaban a yau”.
Ya kara da cewa, rundunar ta NAF na sane da irin babban nauyin da ya rataya a wuyarta na tabbatar da kasar, ta ci gaba da bayar da himma wajen horas da mahimman jami’ai domin samun karfin sarrafa dukkanin manyan jirage da kayan aikin da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta samar.
Da yake magana, Air Marshal Abubakar ya jaddada cewa, karfin aikin sama, wanda ake amfani da dandamalin da aka samu a cikin shekaru 5 da suka gabata, tare da ayyukan sauran hukumomi, ya taimaka kwarai da gaske wajen korar ‘yan ta’addan Boko Haram daga tsohuwar hedikwatar su ta Halifa da ke Gwoza, kamar yadda aka kwato sauran yankunan da ‘yan ta’addan suka mamaye a baya.
Haka zalika, Shugaban ya ce, bama-bamai masu fashewa (IEDs) da ‘yan ta’adda ke amfani da su a cikin duk fadin jihar ta Borno, har ma da sauran kayan aiki da sansanonin horarwarsu duk an tashe su aiki, wanda hakan ya kashe gwiwan ‘yan ta’addan sosai.
Ya kara da cewa, NAF ya kuma ci gaba da bayar da gudummawar ta a cikin ayyukan tsaro na cikin gida a duk fadin kasar da nufin yaki da duk wani nau’i na ta’addanci. Hukumar ta kara kaimi wajen yaki da ‘yan ta’adda da gudanar da sauran ayyukan tsaro a duk fadin kasar kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin’ yan Nijeriya. Ya ba da tabbacin cewa, sayan karin dandamalin jirage, kamar su ‘Super Tucano’, ‘JF-17 Thunder’, da kuma wasu nau’ikan na ‘Unmanned Combat Aerial Behicles (UCABs)’ da kuma wasu karin kayan aiki, babu shakka zai taimaka wa ayyukan NAF.
Shugaban ya yi amfani da wannan damar wajen bayyana godiyarsa ga Babban Kwamandan askarawan Nijeriyar, Shugaba Muhammadu Buhari, saboda samar da kayan aikin da ake bukata ga NAF, don ba ta damar gudanar da ayyukanta. Ya ce, “Za mu iya nuna godiyarmu ne kawai ga goyon bayan Shugaban kasa ta hanyar kasancewa rundunar da masu kwazo tare da matakin kwarewa a dukkan ayyukanmu”.
Har ila yau, Shugaban ya yaba wa Majalisar dokokin kasa, musamman Shugabannin da mambobin majalisar dattijai da kwamitocin majalisar kan Sojin sama, saboda ci gaba da bayar da goyon baya ga hukumar. Ya kuma nuna godiyarsa ga gwamnati da kuma mutanen kirki na Jihar Borno, saboda goyon bayan da suke bayar wa wajen samar wa jami’an NAF da kyakkyawan yanayi don gudanar da ayyukansu. Ya yi alkawarin cewa NAF za ta ci gaba da neman manyan hanyoyi don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, inda ayyukan zamantakewar tattalin arziki za su ci gaba don amfanin jama’a.
A jawabinsa na maraba, Kwamandan ATF, Air Commodore Abubakar Abdulkadir, ya yi amfani da damar don yaba wa shugaban kan ci gaba da jajircewarsa wajen walwala da jin dadin jami’an ATF OPLD, yana mai bayanin cewa hedikwatar NAF ta ci gaba da samar da dukkan abubuwan da suke bukata don tabbatar da cewa jami’ai sun samu tasiri wajen gudanar da ayyukansu. Ya ce, “Za mu ci gaba da rama abubuwan alheri ta hanyar kasancewa masu maida hankali da kuma kwarewar gaske wajen aiwatar da ayyukan da aka ba mu.”
An gudanar da irin wannan liyafar cin abincin na Kirsimeti ga jami’an ATF OPLD da ke aiki a Yola. An gudanar da taron ne a sansanin NAF da ke Yola, inda babban Hafsan ya samu wakilcin daraktan ayyuka na NAF, Air Vice Marshal (ABM) Ayoola Jolasinmi, sannan gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, wanda Shugaban ma’aikatansa, Farfesa Maxwell Gidado, ya wakilta a matsayin babban bako na musamman na karramawa.
A nasa jawabin, Gwamnan ya yaba wa tawagar ATF OPLD a kan gudummawar da suke bayarwa don tabbatar da tsaro ga gwamnatin Jiha, don samar da ayyukan da ake matukar bukata ga ‘yan kasa. Ya kuma yaba wa jami’an saboda sadaukarwar da suka yi wajen yaki da masu tayar da kayar baya tare da kare martabar yankin Nijeriya.
Ya ce, a nata bangaren, Gwamnatin Jihar Adamawa za ta ci gaba da ba da gudummawar da ta dace ga NAF, ‘yar uwarta da sauran hukumomin tsaro don ba su damar yin aiki yadda ya kamata.
Taron, wanda Kwamandan ‘153 Base Services Group’ Yola, Air Commodore Muhammed Yusuf ya hada shi, ya kuma samu halartar wasu jami’an gwamnatin Jihar Adamawa da kuma manyan jami’ai daga sauran hukumomin tsaro a Jihar.
A wajen liyafar cin abincin rana da aka yi wa jami’an sashen Sojin sama na tawagar OPHD a Katsina, shugaban, wanda ya samu wakilcin babban kwamandan rundunar ta musamman (AOC SOC), ABM Charles Ohwo, ya bayyana cewa, yadda yake gudanar da ayyukan sama yayin yaki da masu tayar da kayar baya, yana nuna irin yadda AC OPHD ke bin ka’idojin NAF na kimar nagarta da sanya hukumar a gaban kai.
Ya ce, ci gaba da aiki ta sama da kasa a karkashin OPHD ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka ba su da wurin boya. Ya ce, an rage karfinsu na kai hare-hare kan ‘yan kasa wadanda ba su ji ba ba su gani ba, ta yadda manoma za su iya komawa gonakinsu tare da tabbatar da cewa ‘yan kasa masu bin doka da oda za su iya gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da fargaba ba.
Da yake magana, shugaban ya bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka gabata, NAF ta sami ci gaba matuka ta hanyar shigo da sabbin dandamalin jiragen sama da kuma farfado da wadanda ke kasa, yayin ba da fifiko kan horas da jami’anta. Wasu sabbin jiragen da aka saya, kamar su ‘Mi-171E’, tuni an fara aiki da su a wajen yaki na Arewa maso yamma tare da kyakkyawan sakamako a kan tayin aiki a filin daga.
Don haka ya yaba wa AC OPHD da dukkan rundunonin NAF a Jihar Katsina saboda gudummawar da suke bayarwa ga kokarinsu baki daya. Ya kuma yaba wa ma’aikatan saboda rawar da suka taka da kuma kwarewar da suka nuna wajen gudanar da aikinsu, wanda ya kai ga kubutar da yaran makarantar Kankara da aka sace.