Shugaban kwamitin majalisar Wakilai kan albarkatun Man Fetur, Hon. Ikenga Imo Ugochinyere, ya yaba wa kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPCL), da matatar Dangote, da hukumar kula da albarkatun Man Fetur ta ƙasa (NMDPRA) kan tabbatar da wadatuwar Man fetur a lokacin Kirsimeti.
Ya ce wannan nasara ta biyo bayan aiwatar da dokar harkar Man Fetur (PIA), wadda ta kawo gyara mai alfanu a ɓangaren mai da iskar gas na ƙasa.
- Da Dumi-Dumi: Dangote Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa N899 Kan Kowace Lita
- Dangote Ya Yabi Tinubu Kan Tasirin Yarjejeniyar Musanyar Fetur da Naira
A cewarsa, haɗin gwiwa tsakanin NNPCL da Matatar Dangote ta taka rawa wajen ƙarfafa samar da man Fetur a cikin gida, wanda ya rage dogaro kan shigo da mai daga ƙetare.
Wannan ya ba da damar daidaita rarraba man fetur, tare da magance matsalolin da aka saba fuskanta yayin bukukuwan ƙarshen shekara. Haka kuma, NMDPRA ta taka rawa wajen tabbatar da tsari a kasuwa, wanda ya sa masu amfani da man fetur suka ji daɗin wadatar mai ba tare da cikas ba.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su ci gaba da aiki tare domin tabbatar da ɗorewar ci gaban da aka samu. Ugochinyere ya kuma nuna ƙudurinsa na goyon bayan duk wasu manufofi da za su tallafa wa dorewar wadatar makamashi ga dukkan ‘yan Nijeriya.