A wani bangare na bikin Kirsimeti na bana, wanda ya zo a cikin tashin farashin kayayyaki, a fadin kasar, wata mata musulma, Ramatu Tijjani, ta sake raba kayan abinci da zannuwa da kuma kyautar kudi ga zawarawa Kiristoci 50 a jihar Kaduna.
Daily Nigerian ta rawaito ce wa, matar ta kudurce za ta raba wa zawarawa sama da 200, tana mai cewa hakan wani bangare ne na kokarin inganta zaman lafiya a tsakanin addinai daban-daban.
- NIS Ta Tsawaita Ayyukan Ofisoshinta Zuwa Karshen Mako Domin Yi Wa Mutane Fasfo
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 2, Sun Kwato Makamai A Kaduna
Ta ce an bayar da kyaututtukan ne da nufin sanya musu farin ciki a fuskarsu ta yadda za su kula da marayun su da kuma ba su damar gudanar da bukukuwan cikin farin ciki da jin dadi kamar sauran Kiristocin duniya.
Tijjani ta bayar da gudummawar ne a cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, Sabon Tasha, a jiya Lahadi a Kaduna.
A cewarta, gudummawar ta samo asali ne daga sha’awarta da kuma buƙatar yin tasiri ga rayuwar zawarawa marasa galihu waɗanda suka sha wahala da wariya har ma sun fara fitar da rai da rayuwa.
Ta ce tun shekaru 10 da suka gabata, tana bayar da gudummawar buhunan hatsi, kayan sawa da lemukan sha ga zawarawa Kiristoci da marayu a lokacin Kirsimeti, da bukukuwan Ista da nufin karfafa dangantakar Kiristoci da Musulmi a yankin Arewa.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, matan kiristocin sun kira Tijjani da “Mama” ne saboda kyakkyawar alaka da ta kulla da su wajen karfafa alaka tsakanin Kirista da Musulmi a jihar da ma kasa baki daya.