A lokacin da Laftanar Kanal Abdullahi Hassan Ali, ya zama shugaban Bataliyar Soja ta 181 a Nijeriya, babu abin da mahaifiyarsa ta yi; illa addu’a.
Dalili kuwa, shekara uku da suka wuce ‘yan ta’adda suka kashe ƙaninsa Kaftin Jamilu a a kan bakin aiki a Jihar Katsina. Sannan, a matsayin Ali na guda cikin manyan Dakarun Sojoji a Arewa Maso Gabas, ya sha tsallake rijiya da baya; wajen fafata wa da ‘yan ƙungiyar Boko Haram.
Har ila yau, mahaifinsa ya rasu bayan ya yi ritaya daga aikin Soja. Ko shakka babu, wannan mutuwa ta Ali; ta yi matuƙar tayar wa da mahaifiyar tasa hankali tare da fama mata ciwon mutuwar ɗaya ɗan nata a Katsina da kuma na ‘yarta ita ma da ta haɗu da tsarin mota tare da mijinta duk suka mutu nan take.
Amma Ali, wanda za a iya kira da Sojan-soja; ya samu ƙarin girma a wannan aiki har zuwa matakin Laftanar Kanal a watan Nuwambar 2020, daga nan ne kuma sai aka tura shi ya jagoranci Bataliyar Soja ta 63 a Asaba. Wannan Bataliya, guda ce cikin ƙoƙarin da sojoji ke yi na sake fasalin rundunar haɗin guiwar tsaro (Joint Task Foce), a shekarar 2016, sakamakon yawaitar satar man fetir da aka yi ta faman samu, wanda a duk wata ke tasamma dala biliyan ɗaya.
Batun Rundunar Ta Haɗin Guiwar Tsaro
A wata sanarwar da aka fitar a wancan lokaci, sojoji sun bayyana cewa; an bijro da batun sake fasalin rundunar haɗi guiwar tsaro (JTF) ne, “domin magance matsalar tsaro a yankin Neja Delta, waɗanda suka haɗa da; batun satar fasaha, fasa bututun mai tare da sacewa da kuma sauran ire-iren ayyukan ta’addanci a wannan yanki.”
Wannan runduna ta haɗin guiwa ta haɗa sauran jami’an tsaro daban-daban, amma sojoji su ne ke jagorantar tawagar, duk da cewa kamar yadda al’amarin ya kasance; jami’an ‘yansanda sun kasa jurewa aikin. Dambarwa neman kuɗin man fetir da rikicin ‘yan bindiga da kuma rikicin siyasar cikin gida a yankin, sun haifar da samun sojoji masu zaman kansu, waɗanda suka mallaki muggan makamai da tarin kuɗi da kuma rawar da ‘yan siyasa ke takawa wajen cin karensu babu babbaka a jihohi.
Saboda haka, dangantakar da ke tsakanin waɗannan sojoji masu zaman kansu ko na boge da ita kanta jihar, abu ne mai matuƙar rikitarwa, sakamakon biliyoyin Nairorin da ake samu duk wata a matsayin kuɗin shiga, sannan a matsayinsu na ‘yan tsirari, sun fi sojoji samun manyan makaman yaƙi.
Amma su ‘yan siyasa babu ruwansu, don kawai buƙatarsu ta samun damar satar mai ta biya tar da ci gaba da riƙe madafun ikonsu na siyasa ko mulki, sai kawai suka samar da sojoji masu zaman kansu. Sojojin da suke aikin kula da wurin kuma, an bar su su nema wa kansu mafita ta yadda za su kare jihar da kuma al’ummarta, sannan a gefe guda kuma ga su waɗanda sojoji masu zaman kansu da suke da ƙarfin gaske.
- Yayin Da Hare-hare A Kan Manoma Ke Ta’azzara… ‘Yan Nijeriya Miliyan 18.6 Na Fuskantar Matsananciyar Yunwa
- Turmutsitsin Rabon Tallafi Da Zakka: Yadda Mutum 10 Suka Rasu A Bauchi Da Nasarawa
Yankin da ke da yawan al’ummar kimanin miliyan 31 tare da ƙabilu sama da 40, amma Neja Delta ta zama wata matattara ta talauci, tashin hankali, ta’addanci da kuma rikicin siyasa shekara da shekaru. Sannan, al’ummar yanki za su iya shiga rigimar mata da miji, haka nan al’ummar gari na iya shiga rigimar al’ummar yanki a yi ta faman fafatawa.
A ranar 4 ga watan Maris ne, rikicin tashin hankali ya ɓarke a tsakanin mutanen garin Okuama da Okolobo, a kan gonar kifi.
Tambayoyi…
A ranar Litinin, 14 ga watan Mayu; ya aka yi ofisa wanda ya jagoranci bataliya zuwa Okuama, wanda kuma aikinsa shi ne wanzar da zaman lafiya da kawo daidaito da kuma ayyana aikinsa? shin manufar a kan Okuama ta zargin da ake yi ne na yin garkuwa da mai suna Anthony Abor daga maƙwabtan Okoloba ne (domin ɗaukar fansa a kan wani matashi daga garin Okuama da ake zargin wasu mutane daga garin Okoloba sun kashe shi), a matsayinsa na soja ko wanda ya fara cewa abu, cewa ya yi ɗan sanda? Shin shi ma zai iya kasancewa cikin irin jami’ai da daman da aka sanya su cikin sha’anin harkar siyasa? Ko kuma ya yi hasashen cewa; bayan gazawar yarjejeniyar zaman lafiya da Jihar Delta, shiga tsakani na sojoji ya zama dole; domin kashe wutar?
Rahotannin kafafen yaɗa labarai, sun bayyana cewa; shugabannini Okuama sun tauna goro da wannan jami’i(wanda wasu suka ce, Manjo ne) shi da tawagarsa yayin da suka isa. Saboda haka, a wane lokaci ne tashin hankalin ya ɓarke? Idan al’ummar garin sun ƙi amincewa jami’in ya tafi da shugaban nasu kamar yadda rahotan soja daga Bomada ya sanar, kashe shi shi da tawagarsa tare da ƙwace musu makamansu shi ne mafita?
Saboda haka, bayan dawowarsa a wannan rana, Laftanar Kanal Ali, bai san abin da yake faruwa a Okuama ba. Ya je Kano ya ziyarci mahaifiyarsa da matarsa da kuma ‘ya’yansa su shida, inda ya kwashe makwanni biyu a can; da tunin cewa, sai da sallah kuma zai sake koma ya gan su, idan ya samu dama, amma Okuama nan ne inda yake ransa.
Har ila yau, sojojin da suke jira a kwale-kwale da ke rafin Okuama, sun samu sun tsire bayan kai wa tawagar zaman lafiyar hari, inda aka sanar da Ali abin da ya faru da Manjo da kuma sauran sojoji ukun da suka amince su bishi cikin garin.
A Lura Sosai
Ko kaɗan babu ja a kan abin da wataƙila ya faru, musamman ganin girman yadda ta kasance tsakanin Manjo da yaransa, shi yasa Ali zai tattara tasa tawagar kafin ya tafi? Shin zargin da ake yi cewa, sojojin na amfani da wani kwale-kwale mallakar wani kamfani mai zaman kansa tare da lura cewa; kamfanin na da wata manufa ta bayar da ƙofa wajen cutar da su?
Saboda haka, a cikin yankin da ake fama da wannan rikici, inda sojoji masu zaman kansu ke da bindigogi a kwale-kwale tare da sabbin muggan makamai na zamani, wanda su kansu sojojin ba su da irin su, ta yaya ake tsammanin kwamandan sojojin zai iya yin wani abu a irin wannan rintsi day a samu kansa a ciki a Okuama, inda aka yi wa mutanensa kisan killa tare da ƙwace musu makamai?
Wataƙila, tsananin fushi ne ya sa Ali ya rikice, ya kwashi tawagarsa suka ta fi Okuama. Abin baƙin ciki, wannan ita ce tafiyarsa ta ƙarshe. Haka mutanen da suka yi rantsuwa za su kare su, suka yi musu kwanton ɓauna tare da kashe su.
Don haka, ya kamata a sanya wa wannan aiki na dabbanci ayar tambaya, don hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika. Ana ta kwatanta abin day a afku a Okuama da na Odi a Jihar Bayalsa tun a shekarar 1999, da kuma na Zaki Biam a Jihar Benuwe, shekaru biyu tsakani, inda sojoji suka kashe ɗaruruwan mutane ba bisa ƙa’ida ba.
“Waɗanda suke yin irin waɗancan kwatancen, sun yi kuskure,” Baban Hafsan soja mai ritaya ya faɗa min a makon da ya gabata cewa, “abin da ya faru a Odi da Zaki-Biam shi ne, al’ummomin garuruwan, sun ɓoye waɗanda suka aikata wannan aika-aika amma Okuama gari ne na tsagera.”
A inda aka aikata laifi kamar Okuama misali, dole ne kwamanda ya kasance cikin damuwa kan abin da ogansa zai ce da kuma matsayar Abuja a kan sojoji masu zaman kansu da kuma sauran masu faɗa a ji a yankin. Kasancewa cikin kyakkyawan matsayi tare da tarbar da jihohin suka yi musu, ko shakka babu, ya ƙara ƙarfafa guiwar dakarun sojojin, wanda shi ma hakan bai yi nisa da tinaninsa ba.
Wutsiyar Kare…
Zai yi matuƙar wahala, idan aka samu wasu ‘yan ta’adda suka fara kaɗa wutsiya a cikin al’umma a samu zaman lafiya. Domin kuwa, ga shi yanzu baki-ɗayan al’ummar sunanta ya ɓaci, wanda kuma zai yi wuya ya gyaru a nan gaba.
Kamar yadda Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana ne cewa, za a ci gaba da tuna wa da waɗannan matattu, domin sun cancanci a yi musu adalci. Har ila yau, waƙila kuma lokaci ya yi da za a sake yin nazari a kan rawar da sojiji za su riƙa takawa a cikin rikicin gida.
Wani abin baƙin cikin shi ne, yawan tashe-tsen hankalin da ake yawan samu a sassan faɗin ƙasar nan yanzu, inda yankin Neja Delta ya kasance yanki mafi samun ire-iren wannan, tun bayan yaƙin basasar Nijeriya. A lokacin wannan yaƙi, an lalata yankuna da dama sakamakon kisan gillar da aka yi wa dubban fararen hula, waɗanda ba su ji ba; ba su kuma gani ba.
Kamar yadda masu iya magana suke cewa ne, maciji ba ya saran mumini sau biyu, sannan ba gyara ɓarna da ɓarna, saboda haka; za mu yi ƙoƙarin kaucewa sake afkuwar wannan a nan gaba, ba kawai don gujewa mutuwa da halin da iyalan mamatan ke shiga ciki ba, a’a kawai domin kawai da duk wani abu da ya shafi ko ake da alaƙa da tashin hankali.
Ishiekwene shi ne Babban Editan LEADERSHIP