A daidai lokacin da ake haramar hada-hadar zaben 2023, Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi.
A sakon murnar sabowar shekarar 2023 da tsohon shugaban kasa ya rattaba hannu wanda mai taimaka masa, Kehinde Akinyemi ya raba wa ‘yan jarida, Obasanjo ya siffanta Obi a matsayin mabiyinsa, inda ya ce yana goyon bayan tsohon gwamnan Jihar Anambra a zaben 2023.
Obasanjo ya ce, “Babu daya daga cikin ’yan takarar da ya zama waliyyi sai idan an kwatanta halinsa da fahimtarsa da iliminsa da da’arsa da kuzarinsa da zai iya kawowa da kokarin da ake bukata na tsayawa a mayar da hankali kan aikin, musamman duba da yadda kasar ta tsinci kanta a halin yanzu da kuma gogewa a kan aikin, ni na zabi Peter Obi a matsayin wanda zan mara wa baya a zaben 2023.
“Saura kamar irinmu duka muna da gudummuwar da za mu iya bayarwa wajen ceto Nijeriya daga yanayin da take ciki na bauta.
“Wani abu mai matukar muhimmanci da zan iya fadi game da Obi shi ne, yana iya aiki da ‘yan arewa da kuma ‘yan kudu matukar ya samu nasarar lashe zabe.
“Yana da mutanen da za su iya ja masa kunne matukar ya yi ba daidai ba. Shi matashi ne mai jini jika, haka ma mataimakinsa suna da tarin nasarori da suka cimma a rayuwar al’umma da kuma rayuwarsu na kashin kai.”
A wani bangare na wasikar yana cewa, “Ya zama tilas na rubuta wannan wasika ga dukkan ‘yan Nijeriya, musamman ma matsa, abokaina da ke sassa daban-daban na Nijeriya da na duniya, saboda sauke nauyi da kuma muhimmancin hadin gwiwa wajen yanke hukunci ga ‘yan Nijeriya kanana da dattawa kan babban zabe da za a gudanar a kasa da watanni biyu.
“Shekaru bakwai da rabi da suka gabata ba shakka sun kasance shekaru masu tayar da hankali da damuwa ga yawancin ‘yan Nijeriya. Mun tashi daga saman dutse zuwa kwari.
“Shugabanninmu sun yi iya bakin kokarinsu, amma kokarinsu bai zama mafi alheri ga Nijeriya da ‘yan Nijeriya a gida da waje ba. Yawancin ’yan Nijeriya azaba kawai suke sha a duniya.
“Mu da muke raye ya kamata mu gode wa Allah saboda jin kansa, mu jajirce kan sauran ‘yan watannin wannan gwamnati, sannan mu yi addu’a da yin aiki tukuru don samun kyakkyawar makoma nan gaba da kuma samun ‘yanci da muke tsammani.
“Na yi mu’amala da manyan ’yan takarar kuma na ga abin sha’awa a tattare da su ta wata fuskar, kowannensu ya yi ikirarin cewa yana son yin abin da na yi a lokacin shugabancina da kuma mayar da Nijeriya a babban matsayi a cikin dan karamin lokaci na shugabancina.
“Na ji takaicin yadda akasarin su ba su gane cewa a halin da ake ciki Nijeriya ta fara yin kasa ne tun farkon shugabancina a watan Yunin 1999.
“Ko da yake a wancan lokacin, Nijeriya ta kasance cikin mummunan hali kuma tana daf da rugujewa. Ko a wancan lokacin, Nijeriya ba ta fuskanci matsalar rashin tsaro da ya mamaye ko’ina da rashin shugabanci nagari da gudanar da ayyukan ta’addanci da cin hanci da rashawa da rashin incantaccen tattalin arziki da ke haifar da matsanancin talauci da rashin aikin yi da hauhawar farashin kayayyaki kamar na wannan lokaci ba.”
Shi ma shugaban Kungiyar Ijew na kasa, Cif Edwin Clark ya bi sahun Obasanjo wajen mara baya ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Mista Peter Obi domin ya zama shugaban kasan Nijeriya a zaben da zai guda a wata mai zuwa.
Ya ce idan har Obi ya samu daman zama shugaban kasa, za a samu hadin kai a Nijeriya da kuma sake farfado da kasar.
Goyan bayan Clark yana zuwa ne bayan akwanaki uku da Obasanjo ya nuna goyan bayansa ga tsohon gwamnan Jihar Anambra.
Clark ya bayyana cewa ya kamata duk wanda zai zama shugaban kasa ya kasance mai ilimi da kuma gogewa. A cewarsa, ya kamata a bar yankin kudu maso gabas ya fitar da shugaban kasa da zai gaji Shugaban kasa Muhammadu Buhari, saboda yankin yana da masu ilimi da za su iya jagorancin kasar nan.
Haka shi ma gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom ya bi sahun Obasanjo wajen mara baya ga Obi a zaben da zai gudana a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
A cikin wata nasarwa da ya fitar a ranar Talata da ta gabata dauke da sahannun mai taimaka masa a fannin yada labarai, Terber Akase, gwamna ya siffanta Obi a matsayin mutumin da zai iya magance matsalar tattalin arziki, tsaro da kuma sauran matsalolin da ksar nan take fuskanta.
Sai dai kuma mai magana da yawan kwamitin yakin neman zaben APC, Festus Keyamu ya yi watsi da goyon bayan da Obi ke samu a wurin shugabannin yankin kudu. A cewarsa, duk wannan goyon bayan da Obi ke samu ba za su taba yin tasiri ba.
Keyamo ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita a ranar Talata.
Keyamo ya kara da cewa Obasanjo da Clerk duk sun goyi bayan Atiku Abubakar a zaben 2019, amma kuma bai kai lamari ba.
Ya ce kuri’un da suka bai wa Atiku a 2019 shi ne suke kokarin bai wa Obi a halin yanzu kuma ba zai kai lamari ba.
Shi kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa ko kadan bai damu da goyan bayan da Obasanjo da Clark suka yi wa Obi ba. Ya kara da cewa ‘yan Nijeriya ne kadai za su yanke hukunci kan shugaban kasa a 2023.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata, kakakin yakin neman zaben Atiku/Okowa, Charles Aniagwu ya bayyana cewa duk da shi Clark ya fito daga Jihar Dalta, jiha daya da mataimakin dan takarar jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa ba a hana shi fadan ra’ayinsa.