Maganin Sanyin Mara, Da Rashin Ni’ima
Matar da take fama da sanyin mara ko daukewar sha’awa ko rashin ni’ima ga abin da za ta hada in sha Allah za ta samu waraka.
Abubuwan bukata:
Garin Girfa (cinnamon), Garin kaninfari Clove)
Yadda za a hada:
Za’a samu garin girfa kamar cokali 5 garin kaninfari cokali 7 za a hade waje daya, sai a rika diban rabin karamin cokali ana zubawa a ruwan shayi ana sha sau 2 a rana ayi kamar sati daya.
Za a samu waraka da yardar Allah.
Ciwon Sanyi
Abubuwan bukata:
Hulba, Bagaruwa, Man Habbatussauda
yadda za a hada:
A hada Bagaruwa da Hulba a tafasa su, sai idan ya dan huce sai a zauna a ciki, sannan kuma za a shafa man Habbatussauda a gaban, a sashi kamar yadda za’a yi matsi.
In sha Allah za a samu sauki.