Tao Yuanming, wani shahararren marubuci ne na zamanin daular Dongjin na kasar Sin, wato yau fiye da shekaru dubu 2 da suka wuce. Ya taba siffanta wani wuri mai ni’ima da kwanciyar hankali a cikin wata wakar da ya rubuta. Tun daga wancan lokaci, Sinawa masu dimbin yawa suka fara neman wannan wuri mai ni’ima da kwanciyar hankali, wanda kowa ke alla-alla ya zauna a wurin.
Yau za mu yada zango a birnin Zhangjiajie na lardin Hunan da ke kudancin kasar Sin, inda za mu kara fahimtar ainihin surar yankin yawon shakatawa na Wulingyuan, wanda wuri ne da Tao Yuanming ya taba siffantawa a cikin wakarsa.
Birnin Zhangjiajie da ke yankin tsakiyar kasar Sin na daya daga cikin biranen kasar Sin da suka shahara ta fuskar yawon shakatawa. Kuma an gina gandun dajin shan iska na farko a kasar Sin a wurin, akwai duwatsu masu ban mamaki da kwarran bishiyoyi masu tarin yawa a wurin.
A duk lokacin da aka ambaci sunan Zhangjiajie, wasu su kan yi tambayar cewa, ko dukkan mazauna wurin sunan iyalansu Zhang ne? A Cai, wanda ke yi mana jagora don yin tattaki a birnin Zhangjiajie, ya yi mana karin bayani da cewa, “Dalilin da ya sa ake kiran wannan wuri da sunan Zhangjiajie shi ne, yau shekaru 2200 da suka wuce, da Liu Bang ya kafa daular Xihan ta kasar Sin. Wani janar mai suna Zhang Liang da ke karkashin shugabancin Liu Bang ba ya son ci gaba da kasancewa a kan mukaminsa, sai ya ajiye aiki daga mahukuntan Liu Bang, ya yi tattaki zuwa sassa daban daban. Lokacin da ya isa tsaunin Wuling, wurare masu ni’ima dake wurin sun burge shi matuka, wannan ya sa ya tsai da kudurin ci gaba da zama a nan. Shi babban mutum ne, don haka ya kebe wani yanki mai fadi don ya gina gidaje, tare da ajiye wani dutse a kasa, wanda aka rubuta Zhangjiajie a kai, wato wurin da Zhang Liang yake zaune.”
Yankin yawon shakatawa na Wulingyuan yana arewa maso yammacin lardin Hunan. A Cai, mai yiwa matafiya jagora ya yi mana karin bayani cewa, “Fadin muhimmin bangaren yankin yawon shakatawa na Wulingyuan ya kai misalin murabba’in kilomita 296, wanda ya hada da gandun dajin shan iska na Zhajiajie, yankin kiyaye halittu na tsaunin Tianzishan da yankin kiyaye halittu na kwarin Suoxiyu. Idan matafiya suna son ziyartar yankin yawon shakatawa na Wulingyuan baki daya ba tare da masu jagora ba, to, su kan shafe rabin wata.”
Ranar 7 ga watan Disamba na shekarar 1992, hukumar kula da ilimi da kimiyya da al’adu ta M.D.D. wato UNESCO ta sanya yankin yawon shakatawa na Wulingyuan cikin kayayyakin tarihi na muhallin halittu na kasa da kasa. A Cai ya kara da cewa, “Yanzu muna dab da kofar gandun dajin shan iska na Zhangjiajie, shi ne gandun dajin shan iska na farko a kasar Sin.”
Gandun dajin shan iska na Zhangjiajie ya hada da kauyen Huangshizhai, kwarin Jinbianxi, kauyen Yaozizhai, yankunan Yuanjiajie da na Yangjiajie. A Cai ya yi mana karin bayani a game da kwarin Jinbianxi yana mai cewa, “Akwai wani babban dutse mai suna Jinbianxi a kwarin na Jinbianxi, wanda daya ne daga cikin shahararrun wurare masu ni’ima guda 3 a gandun dajin shan iska na Zhangjiajie. Akwai wani rafin da ke gangara a dab da babban tsaunin, wanda ake kiransa rafin Jinbianxi.”
Mazauna yankin na Zhangjiajie su kan ce, a duk lokacin rani da na damina, ruwa na gangara cikin rafin Jinbianxi. Kwarin Jinbianxi mai tsawon kilomita 5.7 yana da kwane-kwane bisa rafin Jinbianxi, ana shafe misalin awoyi 2 da rabi kafin a kammala kewaya kwarin. Da zummar sassauta gajiyar matafiya, mazauna wurin sun ajiye shinge da dama a gabar rafin Jinbianxi, ta yadda matafiya za su iya jin dadin ganin ruwa dake gangara a rafin, tsuntsaye na waka, kifaye na iyo a rafin, kana kananan jajaye da korran duwatsu suna haskaka a cikin ruwan rafin.
Xiao Qing, wadda ke yi mana rakiya wajen yin yawon shakatawa ta gaya mana cewa, a lokacin da muke kewayawa a kan hanyarmu ta yawon shakatawa, tilas ne mu yi taka tsan-tsan, mu mai da hankali da birran da ke zaune a wurin. Tana mai cewar, “Birran da ke zaune a tsaunin sun saba da mutane sosai. Ba su jin tsoron mutane, a maimakon haka, mu mutane ne kan ji tsoronsu. E, wannan gaskiya ne. Birran kan kwace abubuwan da ke hannunku.”
Duk wanda ya ziyarci kwarin Jinbianxi, ya kan siffanta wannan kwari tamkar dakin nune-nunen zane-zane ko kuma aljannar duniya. A kan hanyarmu ta ziyartar kwarin, wurare masu ni’ima suna ta bayyana a gabanmu. A Cai ya gaya mana cewa, “Kololuwar Muzifeng, wuri mafi ni’ima a kan hanyarmu ta ziyartar kwarin Jinbianxi. Kololuwar Muzifeng ta samu sunanta ne daga siffarta, wadda ta yi kama da yadda mace take rike da yaronta a hannu. Yaron na dogara da mahafiyarsa sosai. Mazauna wurin suna daukar kololuwar ta Muzifeng kamar alamar samun yara ko haihuwa. Ango da amarya ko kuma namiji da matarsa da suka dade ba su samu haihuwa ba, su kan je kololuwar Muzifeng don nuna girmamawa, da zummar samun haihuwa.”
Tsaunuka da kololuwa masu siffofi daban daban, sun sanya mutane kara fahimtar kyan surar muhallin halittu mai ban mamaki. Akwai kuma wani tsauni mai suna Zhu Bajie Bei Xifu, ya kan karfafa kwarewar mutane ta fuskar kagar wani abu. Zhu Bajie na daya daga cikin almajirai 3 na Xuan Zang a cikin “Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong”, wadda tatsuniya ce da ta fi yin suna a cikin adabin tarihin kasar Sin. A karni na 7 bayan haihuwar Annabi Isa A.S., wato lokacin da kasar Sin take karkashin zamanin daular Tang, wani mai bin addinin Buddha mai suna Xuan Zang da aka fi sani da suna mai biyin addidin Buddha na zamanin daular Tang, a takaice ana kiran shi Tang Seng a harshen Sinanci, kuma Seng tana nufin mabiyin addinin Buddha, ya je kasar Indiya domin neman hakikanin ilimin addinin Buddha. Marubucin “Tatsuniyoyin wani biri ne mai wayo da ake kira Sun Wukong” ya danganta wannan labari da ya rubuta abubuwa kan mutane 4, wato Tang Seng da almajiransa 3 a cikin wadannan tatsuniyoyi, inda suka kawar da wahaloli masu dimbin yawa suka ci nasarar neman ilmin gaskiya na addinin Buddha. Ban da wannan, marubucin ya kuma yi nasarar kirkiro wani biri mai wayo kuma maras tsoro da aka fi sani da suna Sun Wukong wanda ya kan yi yaki da mugayen mutane a kowa ne lokaci.
A Cai ya bayyana cewa, “An ce, bayan da Tang Seng da alamajiransa su 4 sun samu ilmin gaskiya na addinin Buddha a kasar Indiya, Zhu Bajie ya koma gida. Wata rana shi da matarsa suka yi tattaki zuwa kwarin Jinbianxi, biri mai wayo wato Sun Wukong ya san wannan labari, ya kuma nemi zolayar Zhu Bajie. Sun Wukong ya yi amfani da dabo ya zama matar Zhu Bajie, kuma ya roki Zhu Bajie da ya dauke shi a bayansa. A kan hanyarsu ta yin tattaki a kwarin Jinbianxi, Sun Wukong ya kara yin nauyi, har ya rikide zuwa wannan dutsen da muke gani a yau. Yau ana zafi sosai, ga shi kuma Zhu Bajie yana rike da wata laima a hannunsa!”
Bisa kwarewar mutane ta fuskar kagar abu, tsaunin ya kasance tamkar Zhu Bajie dake cikin “Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong”. Laimar da yake rike da ita a hannu, a zahiri wani ice ne dake kololuwar tsaunin. Mun ci gaba da tattaki, har sai da muka isa dutsen Jinbianxi, mafi shahara a kwarin Jinbianxi. Rafin Jinbianxi ya samo sunansa ne bisa ga kasancewar wannan dutse.
A Cai ya yi karin bayani da cewa, “Tsayin dutsen Jinbian ya kai mita 348, tsayinsa ya kai babban gini mai benaye 110, ya fi babban ginin ciniki na duniya dake birnin Guangzhou na kudancin kasar Sin tsayi.”
Dalilin da ya sa ake kiran wannan dutse da sunan Jinbian shi ne domin siffarsa ta yi kama da wani nau’in makami mai suna Jinbian da aka taba amfani da shi a zamanin da a kasar Sin. Duk dutsen cike yake da silicon dioxide, don haka a duk lokacin da rana ke faduwa, haskenta kan sanya wannan dutse ya zama kamar zinariya. Wannan na da kyan gani matuka.
Haka kuma a cikin kwarin Jinbianxi, muna iya kallon duwatsu da tsaunuka masu siffofi daban daban, muna jin dadin kara fahimtar kyan surar muhallin halittu mai ban mamaki. Muna kuma iya yin amfani da kwarewarmu ta fuskar kagar wani abu, mun hada tatsuniyoyi da almara na kasar Sin da wadannan duwatsu da tsaunuka tare.
Kwarin Jinbianxi wuri ne da masu son kashe kwarkwaton ido su ziyarta a duk shekara. Ruwan rafin na da tsabta sosai, kuma iskar wuri na da ni’ima. Akwai bishiyoyi da ciyayi masu tarin yawa da suka kewaye kwarin. Haka kuma mutane suna samun kwanciyar hankali yayin da suke kwarin. Musamman ma a lokacin bazara, akwai furanni iri daban daban masu mabambantan launuka a kwarin na Jinbianxi, yayin da a lokacin kaka, launin ganyayen bishiyoyi a wurin kan sauya kamar zinariya, kwarin kan zama kamar wanda aka shafe ko’ina da launin zinariya. (Mai fassarawa: Tasallah Yuan daga CMG Hausa)