Idan aka duba yanayin siyasa, kowa na iya furta albarkacin bakinsa kan wadanda ake ganin za su iya kai wa ga gaci. Amma ‘yan kafafen yada labarai sun fi kowa zakewa da kokarin nuna cewa gwaninsu ne a kan gaba. Sai dai kuma wasu daga cikin ‘yan kungiyar Kwankwasiyya suna wuce gona da iri, musamman wadanda ba sa goyon bayansu da gwaninsu.
A 2019, jama’a sun nuna goyon bayan Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Masu Kwankwaso ne ba don mutanensa sai don an yi na’am da kudirorinsa. Kuma har yau akwai wadanda ba su da wani zabi wajen zabar shugaban Nijeriya sai Kwankwaso saboda, kwarewa, kuzari, da aiki musamman na gina ilmi da ya bai wa matasa, sai dai kuma Allah ne mai bayar da mulki ga wanda yake so, lallai Allah na iya ba shi yana kuma iya hana shi.
Amma a rika sara ana duban bakin gatari, idan an ciza kuma a busa wajen yin la’akari da wadannan abubuwan.
A kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bayyana ceawa ka’idar lashe zaben shugaban kasa ita ce, lashe akalla kashi a 25 na zabe daga kashi biyu cikin uku na jahohin tarayayyar Nijeriya wato ma’ana jihohi ashirin da hudu.
A lissafin siyasar Nijeriya babi na daya wanda ba a fadi a kundin tsarin mulkin Nijeriya ba, shi ne yankin da dan takara ya fito suke zuba zallar kuri’a, yayin da yankin da ba daga can dan takara yake ba nan ake dambarwar samon kashi 25 zuwa 60.
A wani shafi na lissafin siyasar, ana samo wadannan kuri’un na kashi 25 ne ko ma fiye ta hanyar amfani da karfin ‘ya’yan jam’iyyu masu madafun iko a kowacce jiha kama daga kansila da ‘yan majalisu, kwamishinoni har zuwa gwamna, sannan sarakunan sargajiya da malamai da wasu jagororin al’umma, sai kuma tarin kudi da kan yi taron dangi wa neman wannan kuri’un.
Wani shafin siyasar ya nuna yadda iyalan ‘yan takara kan zamo silar samun kuriunsu, misali, matayansa da kan shiga lungu da sako wajen aminan zumunci da biki su samo musu kuri’ar, wani lokacin ma zamantowar matan wasu kabilu ne da bana dan takara ba ko wasu addinai yana da tasiri, misali Abubakar Atiku me mata hudu masu mabambanta yare kuma kowacce za ta janyo kuri’ar a kabilunta, haka ma Bola Ahmed Tinubu mai mata kirista ko ba komai za ta tsakuro masa kuri’un coci.
Kwarewar dan takara wajen shiga lungu da sako tare da yin amfani da wasu yarukan da ba nasa ba ko da kuwa Turanci ne yana sanya zukatan masu jefa kuri’a, mun ga hakan a siyasar Olusegun Obasanjo ta farko a shekarar 1999.
Zubar da kan dan takara a gaban manyan mutane ba kawai zuwa gaishe su a kekashe ba yana laguda zukatan mabiyan babban mutumin su ji an girmama nasu su ma su girmama ka da kuri’a, na taba halartan wani taro inda na ga malamin da ya yi gayyata na zaune a kan keke da yake yana fama da ciwon kafa, amma shi dan takarar da aka gayyata yana tsaye a kansa babu ko rusunawa ko girmamawa. Nan sai ka ji mabiya na ta Allah wadai da dan takara mai yawan girman kai.
Idan wadancan turakun gaskiya ne suna da tasiri a wanne ‘yan kwankwasiya ke da wani kwarin gwiwa a zaben 2023. Masu iya magana na cewa idan an bi ta barawo a bi ta ma bi sahu.
Akwai abun da ake kira kuri’ar raba gardama, ita wannan kuri’a tana fitowa ne daga wani dan siyasar yanki da kan dage ya kafa wata jam’iyya ya tara mata jama’a da ko da ba za ta iya cin kujerar shugaban kasa da kanta ba za ta iya taimaka wa wani ya ci ta hanyar amfani da wasu dabaru kamar haka;
Ko dai narkewa cikin wata jami’yyar da ke neman cikon kuri’un in ya so sai a yi gyaran fuska akida da manufa su zo daya na wucin gadi, za mu ga milsalin hakan ko kwatankwacinsa a hadewar APC na shekarar 2014.
Ko kuma ta tsaya a gefe guda ta kacaccalawa dan takarar yankin da ta fi kwari kuri’a. Misalin hakan shi ne salon da Tinubu da Malam Shekarau suka yi amfani da shi a 2011, inda suka taimaki Jonathan ya kayar da Buhari, lokacin da Malam Shekaru ya tsaya takarar shugaban kasa a ANPP. Ribadu ya tsaya a ACN, suka lalata alkalla kuri’a milyan 2 da ‘yan kai.
Ita ma wannan siyasar kamar saura tana da amfani da rashin amfaninta, amma amfaninta ya fi yawa su ne kamar hakan;
Samar da isasshen lokaci na gina siyasar cikin yanki da hade yankin guri guda kamar yadda muka ga ACN ta yi a kudu maso yamma.
Samar da shugaban siyasa guda daya maimakon daidaiku masu mabambanta muradu da manufa.
Akwai kuma samar da manhaja da alkibla daya ga yankin a hannun ‘ya’yan yankin da suka san ciwon yankin nasu. Kwato wa yankin wasu makudan hakkoki wadanda idan ba kana da alkalumman kuri’a ba, ba za a ba ka ba, wadannan hakkoki sun hada da ababen more rayuwa, kudin gina siyasa da ilmi da sana’o’i.
Akwai kuma batun samar wa siyasar yankin wasu kujeru na dindindin da ba a isa a hana ba, inda su kuma ba su isa su kasa yi wa wanda ya kai su aiki ba.
Bayan takaitattun wadannan nazari, an ya Kwankwaso zai iya kai bantensa a zaben 2023?