Kwanan baya, kungiyar tarayyar Turai(EU) ta gudanar da bincike kan kayayyaki masu amfani da sabbin makamashi na kasar Sin, inda ta yi bincike har sau hudu kan kamfanonin Sin a cikin watanni biyu da suka gabata, kuma wannan ba sabon labari ba ne a shekarun baya bayan nan. To me ya sa EU da Amurka suke matukar son aiwatar da bincike kan kamfanonin Sin a wannan bangare?
Furucin da babban darektan kamfanin Tesla mai samar da motocin dake amfani da wutar lantarki Elon Reeve Musk ya yi ya bayyana mana dalilin, inda ya ce motoci masu amfani da wutar lantarki da Sin ta kera sun fi karfin takara a kasuwannin duniya, amma ya danganta ga yawan haraji ko shingayen da aka sanya mata. Ba a wannan bangare kadai Sin ke fuskantar irin wannan rashin adalci ba, sauran kayayyaki masu amfani da sabbin makamashi su ma batun ya shafe su.
- Xi Ya Gabatar Da Ka’idoji Hudu Don Warware Rikicin Ukraine
- CICPE Na 2024 Dama Ce Ga Kasashen Ketare Ta Fahimtar Kasuwar Sin
An yi ta samun hauhawar farashin na’urorin samar da wutar lantarki ta karfin iska da dai sauran kayayyakin dake alaka da hakan da kasashen Turai suka samar, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da tarwatsa masana’antun samar da kayayyaki masu tushe, kana da matsalar tsarin samar da kayayyaki da dai sauran matsaloli da suke fuskanta. Amma, EU ta dora laifin kan kasar Sin, ta zarge ta da cewa, wai gwamnatin Sin ta samar da tarin tallafi ga kamfanoni masu samar da kayayyaki masu amfani da sabbin makamashi, lamarin da ya gurgunta yanayin takara mai adalci. Ko shakka babu, matakin da EU ke dauka, manufar kariya ce.
Amma, kariyar ciniki ba za ta kai ga kare tsarin masana’antu da ya yi koma baya ba, balle su biya bukatun cikin gida, ko daga karfin takara nasu ba. Fifikon da Sin take da shi a fannin sana’ar samar da kayayyaki masu amfani da sabbin makamashi shi ne karfin kirkire-kirkire babu iyaka da kyautatuwar tsarin masana’antu da isasshiyar takarar kasuwa, babu ruwan tallafi ko kadan. Zai fi kyau kasashen EU da Amurka su bullo da sabuwar hanyar hadin kai don samun moriyar juna a maimakon saka shingaye da yin bincike kan tallafi (Mai zana da rubuta: MINA).