Jam’iyyar APC mai mulki ta gargadi jam’iyyun adawa a Nijeriya ka da su yi zumudin kan kayen da aka yi wa Kamala Harris, a zaben shugaban kasar Amurka, inda ta ce ko shakka babu Shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2027.
A ranar Laraba ne aka sanar da tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump a matsayin wanda ya lashe zaben Amurka, bayan da ya doke Harris a wani gagarumin siyasa da ya jefa fargaba a duniya.
- Mizanin Hajoji Da Hidimomi Da Masana’antun Kasar Sin Ke Samarwa Ya Karu Da Kaso 5.3 Bisa Dari A Watan Oktoba
- Kudirin Sake Fasalin Haraji Ya Raba Kan ‘Yan Majalisar Arewa
Dan kasuwan mai shekaru 78 a duniya ya zama shugaban kasa na 47, kuma shi ne mutum mafi tsufa da ya taba lashe zaben Amurka.
Da yake mayar da martani, sakataren yada labarai na jam’iyyar LP, Obiora Ifo, ya bayyana zaben Amurka da aka sa ido a duk duniya a matsayin gwajin dimokuradiyya na gaskiya.
Yayin da yake bayyana cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) tana da darrusa masu yawa da za ta koya daga zaben Amurka, Ifoh ya ce, abin sha’awa ne ganin yadda Amurkawa masu kada kuri’a suka yi biris da jam’iyya mai mulki, wanda har yanzu shi ne tasiri a zaben Afirka, musamman a Nijeriya.
Shi ma da yake mayar da martini kan zaben Amurkan, mai magana da yawun jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya ce duk da cewa tsarin zaben Amurka yana da sarkakkiya kuma ya yi nisa, yana mamakin yaushe ne Nijeriya za ta kawo karshen shugabanni masu tsatsauran ra’ayi da ke amfani da karfin mulki da jami’an tsaro wajen mulkin kama karya wanda ‘yan adawa kan iya kayar da jam’iyya mai mulki kai tsaye.
Sai dai daraktan yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Bala Ibrahim ya gargadi ‘yan adawa da ka da su bari sakamakon zaben Amurka ya yaudare su, yana mai cewa tsarin zabe a tsakanin kasashen biyu ya sha bamban.
Bala, wanda ya bayyana haka a zantarsa da manema labarai, ya bayyana cewa ba a ko da yaushe karfin mulki ke tasiri ba, lokacin da jama’a suka yi magana da murya daya kamar yadda aka shaida nasarar da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kan shugaba mai ci, Goodluck Jonathan a 2015.
Mai magana da yawun jam’iyyar APC ya bayyana yakinin cewa a lokacin da ‘yan Nijeriya za su fara karbar tukuicin gyare-gyaren tattalin arzikin da shugaban kasa ya yi, za su yaba masa tare da bukatar ya ci gaba da wa’adi na biyu.
Ya ce, “Yadda wannan gwamnatin ta APC ke aiki tukuru, ta kawo sabbin gyare-gyare da sauye-sauye da ke da daci, za mu ci riba sosai a nan gaba.
“Muna sa ran fara ganin amfanin wadannan sauye-sauye kafin lokacin zabe. Wato a kusa da 2026 da 2027. A lokacin ne mutane za su fara yaba wa jam’iyya da shugaban kasa.
“Ba zai yi wuya wani ya fito daga waje ba, musamman wani bare da ya gaza a baya, ko wani baren da ya kasa sawo kan rikicin cikin gidansa kuma ya yi tunanin kayar da mai mulki. Zai yi wahala sosai. Jam’iyyar APC da shugaban kasa suna da masaniya kan wannan zagon kasa da ‘yan adawa ke shirya musu.
“Amma ba wai a ce jam’iyya da shugaban kasa suna barci ba. A’a, suna yin dabarun da za a samu sakamako nan gaba. Don haka, idan muka kai gabar, za mu ga wanda ya fi karfin ketare ta. Kuma ina tabbatar muku da cewa, APC ne za ta lashe zaben shugaban kasa a 2027 a Nijeriya.”