Tun bayan kammala wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai da aka kammala a satin da ya gabata dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Sadio mane, ya bayyana cewa zai bar kungiyar a wannan kakar domin canja wajen buga wasa.
Dama dai kungiyoyi da dama na shirye-shiryen tunkarar kakar badi, sai dai har yanzu ba a fayyace makomar Sadio Mane din ba sai dai rahotanni daga kasar Ingila sun wallafa labarin cewar kungiyar Liverpool ba ta amince da tayin fam miliyan 25 da Bayern Munich ta yi wa dan kwallon Senegal din ba, mai shekara 30 a duniya.
Liverpool ta yi wa Mane farashin sama da fam miliyan 40 ga duk mai son sayen dan kwallon, wanda ya ke kungiyar tun shekara ta 2016 daga Southampton, kuma saura kakar wasa daya yarjejeniyarsa ta kare.
Ana Alakanta Mane da komawa kungiyar Bayern Munich, bayan da Robert Lewawdoski ya ce zai bar kungiyar a kakar nan watakila ya koma buga La Liga a Barcelona a badi idan har burin nasa bai cika ba a wannan karon, haka kuma Munich ba ta da tabbas ko dan wasa Serge Gnabry zai ci gaba da buga wasa a kungiyar a badi ko akasin hakan.
A karshen mako ne Senegal ta doke Benin 3-1 a wasan neman gurbin shiga gasar kofin Afirka, kuma Mane ya ci biyu a karawar, daya a bugun fenariti kuma hakan ne ya sa Mane ya zama kan gaba a yawan ci wa Senegal kwallaye mai 32 a raga a wasa 90 da ya yi mata.
Henri Camara ne a baya mai kwallo 31 ke kan gaba a ci wa Senegal kwallaye a tarihi.