Muhammad Awwal Umar" />

Ko Yanzu Mata Suka Tsaya Takara Za A Fafata Da Su A Rafi -Mairo

HAJIYA MAIRO GAMBO TANKO KAGARA, jigo ce a jam’iyyar APC da ta fafata wajen wayar da kan mata muhimmancin shigar su siyasar da kuma irin nasarorin da hakan ya haifar. A tattaunawarta da Wakilinmu MUHAMMAD AWWAL UMAR ta bayyana cewar jajircewar uwargidan gwamnan jiha, Hajiya Amina Abubakar Sani Bello na kan gaba karfafa guiwar matan da kuma irin alwashin da tasha wajen ganin ta cigaba da kokarin ganin nan gaba matan ma sun fara tsayawa takara a karamar hukumar Rafi. Ga yadda hirar ta kasance:

A shekarun baya idan ana zabe mata ba su cika mayar da hankali akai ba, musamman yadda suke ganin ko su yi zaben ba su cika samun moriyar komai a gwamnati ba, amma a dan wannan lokacin mata a karamar hukumar Rafi sun fara canjawa, shin ya abin yake?

Gaskiya ne a shekarun baya mata ba su faye mayar da hankali kan yin zabe ba, amma bayan zuwan gwamnatin APC maigirma matar gwamnan jiha, Hajiya Amina Abubakar Sani Bello ta kokarta wajen ganin ba a bar mata baya ba, domin kusan shiraruwan da na gabatar yasa mata sun fara sanin anfani gwamnati domin bada jimawa ba na koyar da mata dari biyar sana’o’in hannu, wanda ba su ba ma har mazajensu sun amfana domin a duk lokacin da ka koyar da mace sana’a tamkar ka koyar dubbai dan jama’a da dama za su amfana.

Na biyu bayan uwargidan shugaban kasa ta assasa muna hanyoyin dogaro da kai, uwargidan gwamnan jiha tayi bakin kokarinta wajen taimakawa mata ta hanyar kulawa da su a bangaren kiwon lafiya, cibiyarta ta kafa wajen kula da masu cutar kansa, bada lokacin ga mata masu ciki a lokacin haihuwa tare da kirkiro hanyoyin dogaro da kai ta hanyar horar da su sana’o’in hannu, wanda hakan ya sa nima a matakin karamar hukuma na jajirce wanda yanzu haka dai a Rafi idan na bukaci ganin mace goma to lallai sai ka ga sama da dari a gidana.

Hajiya idan mun yi la’akari da shekarun baya, mata a Rafi ba su cika mayar da hankali ga yin zabe idan ana zabe, sabanin yanzu, ya abin yake ne.

Shi ne na fada ma cewar irin jajircewar uwargidan shugaban kasa, Maman mu Aisha Buhari da kuma uwar mu a nan jiha, Hajiya Amina Abubakar Sani Bello ya zama sanadin wayewar kan mata a Rafi har suka san anfanin siyasa, ina kyautata zaton zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya mata ne suka zuba kuri’a sama da sittin da biyar zuwa saba’in, idan ka zagaya word goma da ke karamar hukumar har wadanda ke cikin karkaru mata sun fi kowa wajen jefa kuri’ar. Ka ga ke nan mu ma mata mun fara sanin anfanin siyasar saboda irin gudunmawar da muke bayarwa, nan gaba kadan ina tabbatar maka cewar za a fafata da mata a fagen siyasar Rafi.

Kina nufin za ku tsaya danganin matan sun fito dan yin takarar siyasa?

Kwarai ma kuwa, domin irin gudunmawar da ni ke samu da goyon bayan maigida na yasa na kara samun kwarin guiwar tallafawa matan, kwanakin baya na yi yunkurin horar da mata dari da ba su tallafi, amma Allah cikin ikonsa da taimakon maigidana na horar da mata dari biyar da tallafin kudi dan yin jari da suka kai dubu dari da turmin zani kowace. To ga ka ga ke nan idan muna samun irin wadannan damammakin ka ga za a kai lokacin da zamu fara tura mata dan yin takarar siyasa wanda ina da yakinin kuma zamu iya cin zabe saboda irin hadin kai da soyayyar da ke tsakanin matan Rafi.

Ganin farin jinin da ki ke da shi a wajen ‘yan uwanki mata da matasa, kina tunanin wannan zai baki kwarin guiwar samun nasarar inganta rayuwar mata da matasa a siyasar Rafi.

Kwarai kuwa, domin lokacin da maigidana, Hon. Gambo Tanko Kagara yake shugabantar karamar hukumar Rafi ya saurari koke-koken mata da matasa, kuma ya bani kwarin guiwar samun nasarar manufofina na inganta rayuwar mata da matasan wanda sakamakon hakan yasa ka ga wannan sakamakon na yau, domin duk da ba mu kan karagar mulki, mata da matasa ba su juya min baya ba, domin na kira su dan su fito su kada kuri’arsu kuma duk mazabar da ka je idan mata ba su rinjayi maza ba to ina tabbatar maka za a yi kan-kan-kan, ka ga ke nan gwamnatin da Hon. Bojoh ya kafa a baya mata da matasa sun gamsu da shi.

Kamar yadda na saba fada a baya, ayyukan da gwamnatin nan tayi a baya kusan mata da matasan sun fi moriya da su domin an samar da ruwan sha, an baiwa mata da matasa jari bayan an horar da su sana’o’in hannu kuma yanzu haka suna cin moriyarsa to ka ga ke nan wannan salon ya taimaka wajen kara min azama da kuma samun nasara a manufofina na inganta rayuwar mata da matasa a karamar hukumar Rafi.

Ganin irin wamnan hubbasar taki ke nan na nuna cewar ke din ma nan gaba za ki iya tsayawa takarar siyasa?

Koda ma ban tsaya ba, lallai sannu a hankali yadda mata suka fara fahimtar anfanin siyasar ina da tabbacin mata a Rafi na gab da fara tsayawa takarar siyasa, domin ziyarar da maigirma gwamna ya kawo a Rafi kwanakin baya, mun nemi mata guda dari da za su mara mana baya amma sai da muka samu mata dari takwas a bayan mu, in ko zamu samu goyon baya ka ga ke nan zamu fara tsayar da mata takarar siyasa nan gaba tunda muna da wadanda suka cancanta din.

A karshe wani shawara za ki baiwa ‘yan uwanki mata ganin ba a bar su baya ba a harkar siyasa?

Na farko a matsayin mu na iyaye da ke kafa tarbiyar farko a rayuwar dan Adam, ya kamata a kowani matakin siyasa a gan mu sahun gaba, sannan samuwar a tafiyar siyasa zai iya kawo karshen yadda ake ta ke mana hakki ko yaushe domin yau mamar mu, uwargidan gwamna, Hajiya Amina Abubakar Sani Bello kowa shaida ne yadda ta ke taka rawa wajen inganta rayuwar mata, domin likita ce da kan ta take karban haihuwa a asibiti, sannan ga cibiyar da ta kafa na tallafawa mata masu dauke da cutar kansar nono ka ga wannan cigaba ne sosai ban cin dubban mata da ta tallafa ma wa wajen ba su jari da dora su akan sana’a ta yadda za su iya dogaro da kan su wanda mu ma a Rafi mun amfana, to ke nan idan mata mu kai rinjaye a siyasa za mu iya samar da hanyoyin zai inganta rayuwar al’ummar kasar nan.

Ina kiran ‘yan uwana da babban murya da cewar mu zama ‘yan sahun gaba wajen tafiyar siyasa, mu tsaya kai da fata wajen ganin an samu zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin kasar nan.

Exit mobile version