Bayan da hukumar dake kula da gasar firimiyar Ingila ta zaftare wa kungiyar Eberton maki 10 sakamakon karya dokokin samun riba da kuma dorewar kasuwanci na gasar Premier, yanzu kallo ya koma kan kungiyoyin Manchester City da Chelsea, wadanda suma ake zargin sun karya irin waccan doka.
Hukuncin shi ne mafi girma na wasanni a tarihin gasar kuma ya bar Eberton a matsayi na 19 a kan teburi inda ta rage da maki hudu kacal, sai dai bayan zartar da hukuncin kungiyar ta ce ya yi bakin ciki da takaicin hukuncin da aka yanke inda ta ce ba a yi mata adalci ba.
- Za A Yi Gwanjon Rigunan Messi Na Gasar Kofin Duniya Ta 2022 Da Kudi Tsagwagwa
- Ko Kyautatawa Na Iya Sa Miji Ya Mallaki Matarsa Bisa La’akari Da Halin Mata?
Eberton ta ce tana da niyyar daukaka kara kan hukuncin kuma kungiyar tana da kwanaki 14 daga ranar da aka yi mata hukuncin domin daukaka kara kamar yadda doka ta bata dama.
Mahukuntan gasar ta Premier sun mika Eberton ga wata hukuma mai zaman kanta a watan Maris, amma ba ta bayyana takamaiman laifin da ake zargin kungiyar da shi ba har lokacin hukuncin.
Kungiyar kwallon kafa ta Eberton ta yi asarar kudi a shekara ta biyar a jere a cikin watan Maris bayan ta ba da rahoton gibin Yuro miliyan 44.7 a kakar wasa ta shekarar 2021 zuwa ta 22. Ana iya barin kungiyoyin Premier su yi asarar da ba ta wuce Fam miliyan 105 cikin shekaru uku kuma Eberton ta yarda cewa ta keta ka’idojin riba da dorewar kasuwanci (PSR) na zangon lokacin da ya kare a 2021 zuwa 2022.